Rasha Ta Yi Tone Tone, An Ji Yadda Kasar Musulunci Ta Iran Ta Fada Tarkon Amurka
- Gwamnatin Rasha ta tuna irin tarkon da Amurka ta dana wa kasar Iran yayin tattaunawa kan shirin kera makamin nukiliya
- Ministan harkokin wajen Rasha, Sergey Lavrov ya ce Iran tana da gaskiya idan ta nuna shakku kan wannan zaman sulhu duba da abin da ya faru a baya
- Ya ce idan har aka cimma yarjejeniya irin ta 2015 tsakanin Amurka da Iran kuma aka aiwatar da ita yadda ya kamata, hakan zai zama babbar nasara
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Russia - Kasar Rasha ta soki shugaban Amurka, Donald Trump, a daidai lokacin da ake jiran tsammani kan yiwuwar tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran karo na biyu.
Ministan harkokin wajen Rasha, Sergey Lavrov, ya tuna cewa a baya Iran ta fada cikin tarkon alkawuran bogi a yarjejeniyar da ta amince ta kulla da gwamnatin Amurka.

Kara karanta wannan
"Abu 1 muke tsoro," Qatar ta tsoma baki kan batun tattaunawar sulhun Amurka da Iran

Source: Getty Images
Lavrov ya tuna irin abubuwan da suka faru da kasar Iran a baya sakamakon yarjejeniyar nukiliya da ta cimma da Amurka, kamar yadda tashar Al-Jazeera ta ruwaito.
Lavrov ya yi gargadi kan alkawuran Amurka
A cewar Lavrov, Rasha na ganin akwai barazana game da alkawura a tattaunawar Amurka da Iran da ake gudanarwa a wannan karon, amma babu hujjoji da za su tabbatar da zargin.
“Mun fahimci hangen da Iran take yi, saboda ta riga ta fada tarkon alkawuran karya a baya, ciki har da yarjejeniyar 2015,” in ji shi.
Ministan na Rasha na magana ne a kan yarjejeniyar nukiliya da aka cimma a zamanin tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama.
Rasha na bibiyar rikicin Iran da Amurka
Ya bayyana cewa Rasha na ci gaba da bibiyar yadda al’amura ke tafiya, yana mai cewa yanayin na iya sauyawa cikin kankanin lokaci, kamar yadda Times of India ta rahoto.

Kara karanta wannan
Duk da kalaman Trump, Iran ta fito da gaskiyar abin ya kawo cikas a tattaunawa da Amurka
Wannan kalamai na zuwa ne yayin da Amurka da Iran ke shirin gudanar da sabon zagaye na tattaunawar tsagaita wuta a kasar Pakistan.
Rahotanni sun nuna cewa mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, da kakakin majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Qalibaf, za su isa Islamabad domin jagorantar tawagoginsu.
To sai dai Iran ta nuna shakku kan wannan tattaunawa bayan da sojojin Amurka suka kwace wani jirgin Iran a kusa da mashigar ruwa ta Hormuz, lamarin da ya kasar ta dakatar da tura tawagarta.

Source: Getty Images
Yadda Iran za ta iya samun nasara
Lavrov ya ce idan har kokarin tattaunawar ya kai ga cimma wata yarjejeniya mai kama da ta shekarar 2015 kuma aka aiwatar da ita, hakan zai zama babbar nasara.
“Idan aka cimma irin yarjejeniyar 2015, ina ganin hakan zai zama gagarumar nasara,” in ji shi.
Qatar ta yi magana kan zaman sulhu
A wani labarin, kun ji cewa Qatar ta bayyana cewa tana ci gaba da tuntubar dukkan bangarorin Amurka da Iran dangane da shirin tattaunawar da za a yi a Islamabad.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Qatar, Majed Al- Ansari, ya ce kasarsa ba ta fatan wannan tattaunawa ta neman sulhu ta rushe.
Dangane da batun rufe mashigar ruwa ta Strait of Hormuz, Majed Al-Ansari ya ce warware wannan matsala ba aikin kasa daya ba ne, illa na dukkan kasash bye.
Asali: Legit.ng
