Daga Karshe Trump Ya Fadi Kasar da Za a Dorawa Alhakin Kashe Mutane a Gabas Ta Tsakiya

Daga Karshe Trump Ya Fadi Kasar da Za a Dorawa Alhakin Kashe Mutane a Gabas Ta Tsakiya

  • Donald Trump ya ce Iran ya kamata ta biya diyya kan asarar rayuka da barna da aka yi wa mutane a Lebanon, Syria, Yemen da Gaza
  • Trump ya ce Amurka za ta nemi Iran ta biya diyya kan rikice-rikicen da ya ce Tehran ta shiga a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Ya ce ya umarci wakilansa su sanya batun biyan diyya cikin duk wata tattaunawa da za a yi nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya kamata a rike Iran da alhakin “barnar da aka yi da mutanen da suka mutu” a Lebanon, Syria, Yemen da Gaza.

Trump ya kara da wannan magana ne bayan kalaman da ya yi a baya cewa Amurka za ta nemi Iran ta biya diyya kan rikice-rikicen da ya ce Tehran ta shiga.

Kara karanta wannan

Trump ya gama barazana ya fadi lokacin kawo karshen yaki da Iran

Trump ya yi magana kan Iran
Shugaba Donald Trump na jawabi a wajen taron G7 Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Litinin, 10 ga watan Agustan 2026.

Kalaman Trump na zuwa ne bayan Iran ta nemi a biya ta diyya kan barnar da Amurka da Isra’ila suka haddasa yayin yakin da aka kwashe watanni ana yi.

Trump ya nemi diyya daga Iran

Donald Trump ya ce Amurka za ta nemi Iran ta biya diyya bayan Tehran ta nemi a mayar mata da kudin barnar da Amurka da Isra’ila suka yi mata yayin yakin.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Iran na neman diyya, amma ya ce Tehran “ba ta taba ambaton biya ta diyya ba” a tattaunawar da aka yi a baya ko kuma ganawar da aka gudanar.

Trump ya ce shi ma yana neman Iran ta biya diyya kan mutanen da ya ce Iran ta kashe ko ta jikkata sosai da bama-baman da ake dasasu a gefen hanya da kuma wasu rikice-rikice.

Kara karanta wannan

Trump ya fusata, ya yi ƙarin haske kan jita jitar cewa suna fama da ƙarancin makamai

Ya kuma hada da iyalan mutanen da aka kashe a harin da aka kai kan jirgin ruwan sojin Amurka USS Cole, da kuma dubban wasu da aka kashe a fagen daga.

An bukaci diyya ga masu zanga-zanga

Trump ya ce Iran ya kamata ta kuma biya diyya ga iyalan masu zanga-zangar da aka kashe a kasar cikin shekaru 50 da suka gabata.

Ya kuma ce ya kamata a biya iyalan daruruwan dubban masu zanga-zangar da ba su ji ba, ba su gani ba” da ya ce Iran ta kashe a cikin shekaru 50 da suka gabata, baya ga mutane 52,000 da ya ce an kashe cikin watanni biyar da suka gabata.

Trump ya umarci wakilansa

Trump ya ce ya umarci wakilansa su tabbatar da cewa batun biyan diyya ya kasance wani bangare na duk wata tattaunawa da za a yi nan gaba.

“Na umarci wakilaina su sanya wannan batu cikin duk wata tattaunawa da za a yi nan gaba.” In ji shi.
Trump ya ce ya kamata Iran ta biya diyya
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

Iran ta nada sababbin kwamandoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa jagoran Iran kuma kwamandan askarawan kasar, Mojtaba Hosseini Khamenei, ya sanar da nada manyan kwamandojin soji shida.

Kwamandojin za su aiki ne a wasu muhimman mukamai a rundunar sojin kasar, Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) da kuma rundunar Basij.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng