Hormuz: Ƴan Damfara Sun Shiga Rigar Iran, Suna Neman Crypto daga Jiragen Ruwa
- An gano wasu masu damfara suna kwaikwayon hukumomin Iran domin karɓar kuɗi daga kamfanonin jiragen ruwa da ke wuce wa ta Hormuz
- Kamfanin kula da haɗarin teku ya ce saƙonnin da ake aikawa na bogi ne, ba daga hukumomin kasar Iran ne ke neman a biya wadannan kudi ba
- Daruruwan jiragen ruwa da dubunnan ma’aikatan teku sun makale sakamakon takunkumin da kasar Iran ta sanya a mashigar Hormuz
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Iran – Wani kamfanin kula da haɗarin zirga-zirgar ruwa mai suna MARISKS ya yi gargaɗi cewa wasu da ba a san ko su wanene ba suna basaja a matsayin hukumomin Iran domin damfarar kamfanonin jiragen ruwa.
A cewar kamfanin, waɗannan mutane suna aika saƙonni ga wasu kamfanonin sufuri na teku, suna neman a biya kuɗin wucewa ta mashigar Hormuz da kuɗin crypto, tare da alƙawarin ba da kariya yayin tafiya.

Source: Getty Images
Aljazeera ta wallafa cewa sai dai kamfanin ya bayyana cewa irin waɗannan saƙonni damfara ne kawai, ba su da alaƙa da gwamnatin Iran ko hukumominta.
An gano masu shiga rigar Iran
Iran International ta wallafa cewa bukatar 'yan damfarar bogin ya ƙara tayar da hankali a cikin masana’antar sufuri ta teku, inda ake fama da ƙalubalen tsaro da rashin tabbas a yankin mashigar Hormuz, wacce ɗaya ce daga cikin manyan hanyoyin jigilar mai a duniya.
Kamfanin MARISKS ya ce:
“Waɗannan saƙonni na musamman damfara ne. Ba hukumomin Iran ne suka aiko su ba."
MARISKS ya kuma bayyana cewa yana zargin akalla wani jirgin ruwa da ya yi yunƙurin fita daga mashigar Hormuz a karshen mako ya fada cikin wannan tarkon damfara, inda aka harbe shi da bindiga.
Ko da yake ba a bayyana cikakken bayani kan harin ba, rahotanni sun nuna cewa lamarin na iya kasancewa sakamakon rashin fahimta ko kuma ƙoƙarin bin umarnin bogi da aka ba su.
Jiragen ruwa na makale a Iran
A halin yanzu, daruruwan jiragen ruwa tare da kusan ma’aikatan teku 20,000 ne suka makale a yankin tekun Gulf, ba su iya wucewa ta mashigar Hormuz ba.

Source: Getty Images
Wannan na zuwa ne bayan da Iran ta sake kakaba wa yankin takunkumi, a matsayin martani ga ci gaba da takunkumin da Amurka ke yi wa tashoshin jiragen ruwan Iran.
Masana sun ce wannan matsala na iya janyo tsaiko a kasuwannin mai da kuma ƙara tashin farashin kayayyaki a duniya, idan har ba a samu warware matsalar cikin gaggawa ba.
Haka kuma, ana ci gaba da kira ga kamfanonin jiragen ruwa da su ƙara taka-tsantsan, su guji amincewa da duk wani saƙo da ba a tabbatar da sahihancinsa ba, musamman waɗanda ke neman kuɗi ta hanyoyin.
Iran ta zargi Amurka da yaudara
A baya, mun wallafa cewa har yanzu kasar Iran ba ta yanke shawarar ko za ta halarci zagaye na biyu na zaman tattaunawar sulhu da Amurka a kasar Pakistan ba bayan an samu matsala a lokacin tsagaita wuta.
Mai magana da yawun Ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei ya ce kasarsa ba za ta manta da yaudara biyu da Amurka ta yi mata baduk da amince da tsakaita wuta domin a hau teburin sulhu.
Ya kuma zargi Amurka da karya yarjejeniyar tsagaita wuta tun daga batun Lebanon, da kuma rufe tashohin ruwan Iran wanda kasarsa ke gani a matsayin cin fuska da take ikonta na kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


