Kasashen Turai 3 Sun Goyi bayan EU Ta Yanke Alaka da Isra'ila kan 'Barnar' Netanyahu
- Kasashen Spain, Slovenia da Ireland sun bukaci kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta tattauna yiwuwar dakatar da yarjejeniyar hulda da kasar Isra’ila
- Ministan harkokin wajen Spain, José Manuel Albares ya bayyana bukatar hakan a ranar Talata kafin taron ministocin harkokin wajen EU a Luxembourg
- Kasashen uku sun aika wata takarda tare ga shugabar harkokin waje ta EU, Kaja Kallas, a ranar Juma’ar da ta gabata, suna rokon ta da dauki mataki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Spain - Ana cigaba da magana kan Kiran da da Firaministan Spain, Pedro Sánchez ya yi na dakatar da yarjejeniyar hulda tsakanin EU da Isra’ila.
Madrid ta sake kawo wannan kudiri bayan karbar bakuncin wani taron shugabannin tarayyar Turai, tana mai kira da a kawo karshen yakin Iran da Amurka.

Source: Getty Images
Ana sa ran kasashen EU za su tattauna bukatar Spain na kawo karshen yarjejeniyar hulda da Isra’ila yayin taron ministocin harkokin wajen da za a yi a Brussels, kamar yadda jami’an diflomasiyya suka shaida wa Euronews.
Kiran raba EU da Isra'ila
Al Jazeera ta rahoto Firaministan Spain, Pedro Sánchez, na zargin Isra’ila da karya dokar kasa da kasa da kuma sharudan yarjejeniyar da ta kulla da tarayyar Turai, inda ya nemi a daina hulda da ita.
Sai dai wannan kira nasa bai kai ga samun matsaya daya daga dukkan kasashe ba, inda ake fatan za su yanke matsaya idan suka tattauna.
Kasashen Ireland da Slovenia suN goyi bayan Spain wajen neman a tattauna yarjejeniyar, suna ganin cewa Isra’ila ta karya dokokin kare hakkin bil’adama ta hanyar karya yarjejeniyar tsagaita wuta.
Ireland da Slovenia sun zargi Isra'ila da kara jawo tashin hankali a West Bank, hare-hare kan fararen hula a Lebanon da kuma amincewa da hukuncin kisa ga Falasdinawa a majalisar kasar.

Source: Getty Images
Hanyar yanke alakar EU da Isra'ila
Dakatar da yarjejeniyar gaba daya na bukatar matsaya guda daga dukkan kasashe, kamar yadda Kaja Kallas ta bayyana, duk da cewa ba a fayyace hakan a fili a yarjejeniyoyin EU ba.
A halin yanzu, babu cikakken goyon baya daga kasashen tarayyar Turai kan dakatar da yarjejeniyar, in ji wani jami’in diflomasiyya.
Rahoto ya nuna cewa kasashe kamar Germany da Italy, wadanda suka saba adawa da wannan kudiri, ba su sauya matsayarsu ba har yanzu.
Barazanar da EU ta yi wa Isra'ila
A watan Satumban 2025, Hukumar Tarayyar Turai ta gabatar da shawarar dakatar da wani bangare na yarjejeniyar, musamman bangaren kasuwanci, yayin da yakin Gaza ke ci gaba.
Shugabar hukumar, Ursula von der Leyen, ta gabatar da wannan shawara, amma ta fuskanci irin wannan adawa daga kasashen EU.
Za a kama Netanyahu a Hungary
A wani labarin, kun ji cewa sabon Firaministan kasar Hungary ya yi alkawarin cafke Firaministan Isra'ila idan ya kuskura ya taka kasar shi.
Péter Magyar ya yi wa Netanyahu gargadin ne kwanaki kadan bayan ya lashe zabe, inda ya kayar da babban abokin Donald Trump.
Kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya (ICC) ce ta bukaci a kama Benjamin Netanyahu bisa aikata kisan kare dangi ga Falasdinawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


