Kwankwaso Ya Zargi Jingir da Rura Wutar Rikici bayan Kalamansa kan Muslim Muslim
- Sanata Rabiu Kwankwaso ya shiga cikin jerin wadanda suka soki kalaman Sheikh Sani Yahaya Jingir kan tikitin Musulmi da Musulmi a zaɓen 2027
- Tsohon gwamnan Kano wanda shi ne dan takarar mataimakin shugaban Kasa a NDC ya ce irin waɗannan kalamai na iya raba kan al’umma
- Sanata Kwankwaso ya ce mutanen Kano ba sa goyon bayan kalaman Jingir, yana mai kira ga shugabannin siyasa da addini da su ƙarfafa haɗin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tsohon gwamnan Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Kwankwaso, ya yi Allah wadai da kalaman malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Yahaya Jingir.
Shiekh Jingir ya yi kalamai masu zafi a yayin da ya ke nuna goyon bayansa kan ci gaba da amfani da tikitin Musulmi da Musulmi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Source: Facebook
Kwankwaso ya bayyana takaicin kalaman da Sheikh Jingir ya yi amfani da su ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, inda ya ce kalaman Jingir na iya raba kan al’umma.
Kiran Kwankwaso ga kalaman Sheikh Jingir
Kwankwaso, wanda ke takara tare da Peter Obi a NDC ya kuma yi kira ga shugabannin siyasa da na addini da su mayar da hankali wajen inganta haɗin kai da sulhu tsakanin al’umma.
Kwankwaso ya ce yana matuƙar damuwa da kalaman da Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi a wani taro da aka gudanar a Kano a ƙarshen makon da ya gabata.

Source: Facebook
Ya ce:
“Na damu matuƙa da kalaman da Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi a wani taro a Kano a ƙarshen wannan mako. A wannan lokaci mai muhimmanci a tarihin ƙasarmu, dole ne a yi Allah wadai da kalaman da ke ƙarfafa rarrabuwar kai da rashin haɗin kai."
Yadda Sheikh Jingir ya jawo magana
Sheikh Jingir ya janyo ce-ce-ku-ce ne bayan ya bayyana goyon bayansa ga ci gaba da amfani da tikitin Musulmi da Musulmi a zaɓen 2027.
Malamin ya yi wannan magana ne a yayin bikin auren gata da aka yi a jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Yusuf, inda ya munana kalamai ga Kiristoci.
Da yake mayar da martani, Kwankwaso ya ce shugabannin addini da na siyasa suna da alhakin guje wa kalaman da za su iya ƙara raba kan ’yan Najeriya.
Ya ce:
“Abu ne mai tayar da hankali musamman idan aka ji irin waɗannan kalamai daga shugaban addini mai matsayi da tasiri irin na Sheikh Jingir."
“Mutanen kirki na Kano ba sa amincewa ko goyon bayan waɗannan kalamai masu raba kan jama’a. Shugabannin siyasa da na addini suna da babban nauyi na tabbatar da gaskiya, ƙarfafa haɗin kai da kuma samar da sulhu."
Tsohon Minista ya dura kan Jingir
A baya, mun kawo labarin cewa jakadan Najeriya a kasar South Africa, Femi Fani Kayode, ya yi wa Sheikh Sani Yahaya Jingir martani kan goyon bayan muslim-muslim da kalaman da ya yi amfani da su.
Femi Fani Kayode ya yi martanin ne bayan Sheikh Jingir ya kira ga musulmi su sake goyon bayan tikitin muslim-muslim a zaben 2027 tare da kausasa aharshe wajen cewa dole a nuna cewa an fi kafiran Najeriya yawa.
Wadannan kalamai sun jawo martani masu zafi inda ake ganin an shigar da addini cikin kazamar siyasa, wanda zai iya jawo rabuwar kai da zurfafa kiyayayya a tsakanin Musulmi da Kiristocin kasar nan.
Asali: Legit.ng


