Yajin Aiki: Jerin Jami'o'i 20 da ASUU Ta Fara Shirin Dakatar da Harkokin Karatu a Najeriya

Yajin Aiki: Jerin Jami'o'i 20 da ASUU Ta Fara Shirin Dakatar da Harkokin Karatu a Najeriya

  • Kungiyar ASUU ta ƙasa ta umarci jami’o’in jihohi kusan 20 su fara yajin aiki na sai baba-ta-gani cikin makonni biyu masu zuwa
  • ASUU ta bayyana cewa ta dauki wannan matakin ne saboda gaza aiwatar da yarjejeniyar 2025 tsakanin gwamnati da kungiyar
  • Shugaban ASUU na kasa, Christopher Piwuna, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, bayan taron majalisar zartarwa NEC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umarci jami’o’in jihohi akalla 20 a fadin kasar da su fara yajin aiki na sai baba-ta-gani cikin makonni biyu masu zuwa.

ASUU ta dauki wannan mataki ne saboda abin da ta bayyana a matsayin rashin tsari wajen aiwatar da sabuwar yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2025.

Christopher Piwuna
Shugaban kungiyar ASUU ta kasa, Farfesa Christopher Piwuna yana hira xa yan jarida a Abuja Hoto: @thecompasshub
Source: Twitter

The Cable ta ruwaito cewa ƙungiyar ta ce jami’o’in da abin ya shafa za su fara da ba gwamnatocin jihohinsu wa’adin kwanaki 14 ga kafin su shiga yajin aikin domin neman a cika alkawuran da ke cikin yarjejeniyar.

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, Jami'ar Kano ta faɗi gaskiya kan zargin Sarki Sanusi II ya faɗi jarabawa

Shugaban ASUU na kasa, Christopher Piwuna, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, bayan taron majalisar zartarwa ta kasa (NEC) na kungiyar da aka gudanar a Jami’ar Abuja.

ASUU ta nuna rashin jin dadi

Piwuna ya ce NEC ta tattauna kan halin da kungiyar take ciki, musamman bayan da aka sanya hannu kan yarjejeniyar 2025 tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU.

Sai dai ya ce kungiyar ba ta gamsu da yadda ake aiwatar da yarjejeniyar ba, musamman abin da ta kira “haphazard implementation”, wato aiwatarwa ba tare da tsari ko daidaito ba.

ASUU ta kuma nuna rashin jin dadinta kan abin da ta bayyana a matsayin rashin kulawar gwamnatin tarayya wajen sakin tallafin da ake bukata domin tabbatar da cikakken aiwatar da yarjejeniyar.

An kulla yarjejeniyar bayan shekaru 16

Yarjejeniyar 2025 ta biyo bayan dogon rikici da ya shafe kusan shekaru 16 ba tare da samun cikakken matsaya kan aiwatar da wasu bukatun malaman jami’o’i ba.

Kara karanta wannan

Jami'ar ABU ta waiwayi Farfesa Abdullahi, wanda aka ce yana da PhD 5, MSc 5 da digiri 7

A ranar 14 ga Janairu ne gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar da ASUU domin magance wasu matsalolin da suka dade suna haddasa yajin aikin jami’o’in gwamnati a Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa kusan jami’o’in jihohi 10 ne kawai suka aiwatar da yarjejeniyar gaba daya, yayin da sama da 57 ke cikin halin rashin tabbas.

Wannan ne ya kara matsa lamba kan ASUU wajen daukar matakin yajin aiki domin tilasta a aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata, in ji rahoton Punch.

Sunayen jami’o’i 20 da za a shiga yajin aiki

Jami’o’in da ASUU ta umarta su ba da wa’adin kwanaki 14 kafin fara yajin aikin sun hada da:

  1. Jami'ar jihar Nasarawa da ke Keffi
  2. Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida, Lapai
  3. Jami'ar Kimiyyar likitanci ta Ondo
  4. Jami'ar jihar Gombe
  5. Jami'ar jihar Plateau
  6. Jami'ar Adekunle Ajasin, Akungba
  7. Jami'ar Ambrose Alli, Ekpoma
  8. Jami'ar kimiyya da fssha ta Olusegun Agagu, Okitipupa
  9. Jami'ar jihr Abia
  10. Jami'ar ilimi da koyar da kasuwanci, Akamkpa
  11. Jami'ar ilimi ta Emmanuel Alayande, Oyo
  12. Jami'ar jihar Kaduna
  13. Jami'sr Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote Kano, Wudil
  14. Jami'ar Northwest ta Kano
  15. Jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar Enugu
  16. Jami'ar Jihar Imo
  17. Jami'ar Neja Delta
  18. Jami'ar Afirka da ke Toru-Orua
  19. Jami'ar Kimiyyar Likitoci ta Bayelsa
  20. Jami'ar jihar Taraba da ke Jalingo.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke kwandon alheri a jami'o'in jihar 2

ASUU.
Tambarin kungiyar malaman jami'o'i ta kasa watau ASUU HOTO: ASUU Nigeria
Source: Twitter

An karrama daliban jami'o'i 20 a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin Stransact zai karrama dalibai 100 mafi hazaka daga manyan jami'o'i 20 na Najeriya saboda bajintar da suka nuna.

Dukkan dalibin da aka zaba zai samu N100,000, takardar karramawa da kuma damar shiga shirin bunkasa rayuwar dalibai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262