Kwana 1 kafin Ci Gaba da Yaki, Shugaban Amurka Ya Fadi Abin da Yake Tsammani daga Iran

Kwana 1 kafin Ci Gaba da Yaki, Shugaban Amurka Ya Fadi Abin da Yake Tsammani daga Iran

  • Shugaba Donald Trump ya ce yana tsammanin Amurka za ta cimma yarjejeniya mai kyau da kasar Iran kafin karewar wa'adin tsagaita wuta
  • A gobe Laraba, 22 ga watan Afrilu, 2026 yarjejeniyar tsagaita wuta ta makonni biyu da aka cimma tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila za ta kare
  • Trump ya yi ikirarin cewa iran ba ta da sauran karfin soji da za ta iya ci gaba da yaki da Amurka, don haka sulhu ne kadai zabin da ya rage

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

United states - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa yana da yakinin cewa kasarsa za ta cimma “kyakkyawar yarjejeniya” da Iran domin kawo karshen yakin da ya shafe makonni ana yi.

Shugaba Trump ya fadi hakan ne jim kadan bayan ya sake jaddada cewa ba zai tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da za ta kare gobe Laraba ba.

Kara karanta wannan

"Babu lokaci," Trump ya sake maganar tashin hankali, ya mika zabin da ya rage ga Iran

Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump na shirin hira da yan jarida kafin ya hau jirgi zuwa Virginia Hoto: Win Mcnamee
Source: Getty Images

Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da tashar CNBC a shirin “Squawk Box”, inda ya ce yana sa ran samun sakamako mai kyau daga zagaye na biyu na tattaunawar zaman lafiya da Iran.

“Ina ganin ba su da wani zabi,” in ji Trump, yana mai nuni da cewa Iran za ta koma teburin tattaunawa domin hakan shi ne mafi alheri ga kasar.

Donald Trump ya yi ikirarin raunana karfin Iran

Shugaban ya kara da cewa Amurka ta riga ta lalata muhimman bangarorin karfin sojin Iran, ciki har da rundunar ruwanta da ta sama.

“Mun rusa rundunar sojojin ruwansu, mun rusa rundunar sojojin sama, mun kuma kawar da shugabanninsu,” in ji shi

Sai dai Shugaba Trump ya amince cewa kawar da shugabannin ya kawo wasu kalubale, amma ya ce sababbin jagororin Iran sun fi nuna hankali wajen yanke hukunci.

“Gaskiya ne, mun cire shugabanninsu, wanda hakan ya 'dan rikitar da al’amura ta wata fuska, amma wadannan shugabannin na yanzu sun fi hankali,” in ji shi.

Kara karanta wannan

"Abu 1 muke tsoro," Qatar ta tsoma baki kan batun tattaunawar sulhun Amurka da Iran

Amurka na tunanin ta sauya Gwamnatin Iran

Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa abin da ya faru a Iran na iya zama kamar sauyin gwamnati, ko da yake bai fito fili ya ce hakan ne manufarsa ba tun farko

“Wannan sauyin gwamnati ne, ko da kuwa me za ka kira shi, duk da ban bayyana cewa zan yi hakan ba, amma ya faru ta wata hanya,” in ji shi.
Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei.
Jagoran addini na kasar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Lokacin da aka tambaye shi ko zai tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta domin bai wa tattaunawar karin lokaci, Trump ya ce ba ya son yin hakan.

Idan dai ba a tsawaita wa'adin tsagaita wuta ba kuma ba a cimma matsayar sulhu tsakanin kasashen ba, Amurka na Iran na iya komawa fagen yaki a karo na biyu.

Trump ya sake yi wa Iran barazana

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya sake yin barazanar ci gaba da kai hare-hare Iran matukar ba a cimma yarjejeniyar zaman lafiya ba.

Kara karanta wannan

Duk da kalaman Trump, Iran ta fito da gaskiyar abin ya kawo cikas a tattaunawa da Amurka

Shugaban na kasar Amurka ya ce a halin yanzu babu wani lokaci da ya rage, yana mai gargadin cewa dole ne kasar Iran ta dauki mataki cikin gaggawa.

Trump ya kuma bayyana cewa sojojin Amurka sun yi amfani da lokacin tsagaita wuta wajen sake sabunta makamai, kuma yanzu a shirye suke su koma kai hare-hare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262