Tirkashi: Trump Ya Bayyana Aiki Mai Wahala da Amurka Za Ta Yi a Iran
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sake yin tsokaci kan sinadarin Uranium da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta inganta
- Trump ya bayya na cewa hare-haren da Amurka ta kai a shekarar da ta gabata sun lalalta wuraren nukiliyar Iran
- Shugaban na Amurka ya nuna cewa akwai aiki wanda zai ci lokaci kuma mai wahala wanda za a gudanar kan wuraren nukiliyar Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan kwaso sinadarin Uranium da aka inganta daga Iran.
Trump ya bayyana cewa kwaso sinadarin Uranium daga Iran da Amurka za ta yi zai kasance abu ne “mai tsawo” kuma “mai wahala”.

Source: Getty Images
Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Litinin, 20 ga watan Afirilun 2026.
Wane aiki mai wahala za a yi a Iran?
Trump ya bayyana cewa aikin zai kasance mai wahala ne biyo bayan hare-haren da Amurka ta kai kan wuraren nukiliyar Tehran a shekarar da ta gabata.
“Operation Midnight Hammer ya alata wuraren ƙurar nukiliya a Iran baki daya. Don haka, tono shi zai kasance aiki mai tsawo da wahala.”
- Donald Trump
Donald Trump na magana kan Uranium na Iran
Jaridar Vanguard ta ce Shugaban na Amurka yakan yi amfani da kalmar “ƙurar nukiliya” akai-akai don yin ishara da tarin sinadarin Uranium da Iran ta inganta, wanda Amurka ke zargin Iran da adana shi domin kera bam.
Amma kuma wani lokacin ya kan yi amfani da kalmar don yin nuni ga abubuwan da suka yi saura bayan hare-haren da Amurka ta kai wa cibiyoyin nukiliyar Iran a watan Yunin shekarar da ta gabata.
Trump ya ce za a kwashe Uranium daga Iran
Shugaban mai shekaru 79 ya jaddada cewa lallai za a mayar da tarin sinadarin uranium ɗin na Iran zuwa yankin Amurka, duk da cewa ma’aikatar harkokin wajen Iran ta musanta kowane irin shiri na hakan.

Kara karanta wannan
Yawan surutun shugaban Amurka, Trump ya jawo masa martani mai zafi daga kasar Iran
Amurka da Isra'ila sun ƙaddamar da hare-haren haɗin gwiwa a kan Iran a ranar 28 ga Fabrairun 2026 don kawar da abin da Isra'ila ta bayyana a matsayin “barazana mai wanzuwa” da shirin nukiliyar jamhuriyar Musulunci ya haifar.

Source: Getty Images
Jami'an Isra'ila sun ce Tehran ta ƙara ƙaimi wajen neman mallakar makamin nukiliya tun bayan ƙarshen yaƙin kwanaki 12 na watan Yunin da ya gabata, wanda Isra'ila ta ƙaddamar kuma ya haɗa da harin bama-bamai na Amurka a kan cibiyoyin nukiliya guda uku, har da masana'antar sarrafa sinadarin uranium.
Trump ya magantu kan yarjejeniya da Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi tsokaci kan yarjejeniyar da za a kulla da Iran.
Shugaba Trump ya bayyana cewa Amurka za ta kulla yarjejeniya mai kyau da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Donald Trump ya yi iƙirarin cewa yarjejeniyar da Amurka ke ƙullawa da Iran za ta fi JCPOA kyau nesa ba kusa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
