Yadda Rikicin Iran Ya Buɗe Kasuwar Man Najeriya, Ƙasashen Turai Sun zo Neman Agaji

Yadda Rikicin Iran Ya Buɗe Kasuwar Man Najeriya, Ƙasashen Turai Sun zo Neman Agaji

  • Najeriya ta fitar da sama da lita biliyan ɗaya na man jiragen sama zuwa Turai cikin kwanaki 50 bayan an fara ganin ƙarancinsa
  • Matatar man Ɗangote ce ke jagorantar wannan babban ci gaba da Najeriya ke samu a bangaren mai, kuma ita ta fitar da kayan
  • Tun bayan fara yaƙin ta Tsakiya, aka tilasta wa Turai neman madadin masu samar da mai bayan an rufe mashigar Hormuz

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Nigeria – Yayin da Turai ke fuskantar barazanar ƙarancin man jiragen sama kafin lokacin hutun bazara, hankalinta ya karkata zuwa sababbin masu samar da mai.

Wannan al'amari ya sa Najeriya ta zama muhimmiyar madadin gaggawa a ɓangaren samar da man jiragen sama a duniya bayan datse mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

A karon farko, matatar Dangote ta hako 'danyen mai a Najeriya

Dangote ya jagoranci Najeriya wajen samar wa Turai man jirgin sama
Alhaji Aliko Dangote, ma'aikaci a matatar mai Hoton: Dangote Industries
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa sababbin bayanai sun nuna cewa Najeriya ta fitar da kusan lita biliyan 1.1 na man jiragen sama zuwa Turai cikin watanni biyu kacal.

Likkafar Najeriya ta ɗaga a kasuwar mai

Trust Radio ta wallafa cewa wannan ci gaban da Najeriya ta samu ya samo asali ne musamman daga matatar Dangote da ke Legas.

Rahotanni sun nuna cewa an fitar da tan 456,000 a watan Maris, 2026 sannan tan 420,000 a watan Afrilu, 2026 wanda ya kai sama da lita biliyan ɗaya a cikin kwanaki 50 kacal.

Masana sun ce wannan ya nuna yadda Najeriya ke ƙara zama muhimmiyar ƙasa a kasuwar makamashi ta duniya, musamman bayan rikicin Gabas ta Tsakiya

Abin da ya haɓaka kasuwar man Najeriya

Rahotanni sun ce kasashen Turai sun dawo kan Najeriya ne sakamakon rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, musamman tangardar jigilar mai ta mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Yakin Iran da Amurka: Kasashen Turai za su shiga gagarumar matsala nan da mako 6

Wannan mashigar ruwa da ta ratsa ta Iran, ta nan ne ake jigilar kusan kashi ɗaya cikin biyar na man da ake amfani da shi a duniya baki daya.

Tun bayan fara yaƙi da Iran aka rufe mashigar Hormuz
Shugaban Masar Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: Masoud Pezeshkian
Source: Facebook

Tun bayan fara rikici tsakanin Amurka da Iran, an samu tsaiko a zirga-zirgar mai, lamarin da ya janyo matsin lamba a kasuwannin duniya da tashin farashi.

Turai da ke dogaro da shigo da kusan 30% na man jiragen samanta, ta fara jin tasirin wannan rikici kai tsaye, wanda ya sa neman mafita.

Wannan na daga cikin dalilan da ya sa ƙasashen Turai suka karkato da hankulansu ga makamashin da ke Najeriya domin cike giɓin.

Farashin mai ya tashi a Najeriya

A baya, mun wallafa cewa yan kasuwar man fetur sun yi gargadin cewa farashin fetur na iya tashi zuwa kusan N1,000 kan kowace lita sakamakon tashin farashin danyen mai a duniya.

Tashin farashin danyen mai zuwa sama da dala 70 kan kowace ganga ya zo ne a daidai lokacin da matatar Dangote ta kara farashin fetur daga N739 zuwa N839 a Najeriya.

Kungiyoyin ’yan kasuwa sun ce idan wannan yanayi ya ci gaba, masu saye da masu sayarwa za su fuskanci karin matsin tattalin arziki a sassa daban-daban na kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng