Kano Ta Karyata Sanya Wasu Dattawa a Auren Gata, Ta ba Limaman Juma'a Umarni

Kano Ta Karyata Sanya Wasu Dattawa a Auren Gata, Ta ba Limaman Juma'a Umarni

  • Gwamnatin Kano ta ba limaman masallatan Juma’a umarni kan yi wa jama’a bayani kan aurar da matasa, tare da karyata labaran ƙarya
  • Kwamishinan ya ce hotunan wasu dattawa da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta ba su nuna waɗanda aka aurar ba, domin tsoffin jami’an Hisbah ne.
  • Kungiyar matasan masallatan Juma’a ta yaba wa Gwamna Abba Yusuf, tare da bayyana goyon bayanta ga sake zaɓensa a zaɓen gwamnan Kano na 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Gwamnatin Kano ta umarci limaman masallatan Juma’a a faɗin jihar da su wayar da kan al'umma kan auren gata.

Gwamnatin ta umarci malaman su yi amfani da wa’azinsu wajen karyata bayanan ƙarya game da shirin aurar da jama’a.

Abba Kabir ya umarci limaman Juma'a kan auren gata
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano yana jawabi. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayar da umarnin yayin ganawarsa da ƙungiyar matasan masallatan Juma’a, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya tona yadda yan siyasa ke gwara yan Najeriya da sunan addini

Rawar da malamai ke takawa cikin al'umma

Waiya ya ce shugabannin addini, musamman limamai da malaman Musulunci, suna da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da dakile yaɗuwar bayanan ƙarya.

Ya bayyana damuwarsa kan yadda ake yaɗa hotunan wasu dattawa a kafafen sada zumunta, ana gabatar da su ƙarya a matsayin waɗanda suka amfana da shirin.

A cewarsa, wasu daga cikin dattawan da aka nuna a hotunan tsoffin jami’an Rundunar Hisbah ne da suka yi ritaya, kuma sun halarci taron.

Kwamishinan ya jaddada cewa bai kamata a ɗauki halartar waɗannan dattawa a wajen taron a matsayin alamar cewa an aurar da su cikin shirin ba.

Ya bukaci limamai da sauran shugabannin addini su riƙa bai wa al’ummarsu sahihan bayanai game da shirin, tare da hana yaɗuwar jita-jita da bayanan yaudara.

Umarnin Abba Kabir ga limaman masallatan Juma'a
Taswirar jihar Kano da aka gudanar da auren gata. Hoto: Legit.
Source: Original

Muhimmancin auren gata a Kano

Waiya ya ce shugabannin addini suna da damar taimaka wa gwamnati wajen bayyana manufofin shirye-shiryenta ga jama’a, musamman waɗanda ke tallafa wa iyalai.

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, Jami'ar Kano ta faɗi gaskiya kan zargin Sarki Sanusi II ya faɗi jarabawa

Ya ƙara da cewa irin waɗannan shirye-shirye na taimakawa wajen ƙarfafa zamantakewa da haɗin kan al’ummar Kano.

Tun da farko, shugaban ƙungiyar, Imam Gwani Sani Tilo, ya yaba wa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf kan shirye-shiryen inganta rayuwar mazauna Kano.

Ya musamman yaba da shirye-shiryen da suka shafi harkokin Musulunci da jin daɗin al’ummar Musulmi a faɗin jihar, cewar Daily Post.

Tilo ya kuma bayyana dalilin da ya sa ƙungiyar ta bar tsohuwar ƙungiyar siyasa da take tare da ita, inda ta koma jam’iyyar APC tare da Gwamna Yusuf.

Auren gata: Sakon Abba ga malamai, sarakuna

Kun ji cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mika sako ga sarakunan gargajiya da malaman addini bisa irin gudunmawar da suka bayar.

A ranar Asabar 8 ga watan Agusta, 2026 ne gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi shagalin bikin auren mutane 3,000 a jihar.

Gwamnan ya kuma tura sako ga angwaye da amare da suka rabauta da shiga wannan tsari ganin za su fara sabuwar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.