Trump Ya Ajiye Takama, Ya Mika Bukata ga Iran Yana So a Biya Masa Ita
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya bukaci Iran ta biya diyya kan mutanen da ya ce kasar ta kashe a tsawon shekaru
- Trump ya ce Amurka za ta nemi a biya ta diyya kan asarar da Iran ta jawo cikin shekaru 50, yayin da ake ci gaba da tattaunawa
- Iran ta sanya biyan diyya da kawo ƙarshen takunkuman Amurka cikin sharudan sake buɗe mashigar da ke da ake takaddama a kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington DC – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bukaci Iran ta biya diyya kan mutanen da ya ce kasar ta kashe, yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan sake buɗe mashigar Hormuz.
Rahoto ya nuna cewa Trump ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin da yake magana da manema labarai a Fadar White House.

Source: Getty Images
Trump ya nemi Iran ta biya diyya
Al Jazeera ta wallafa cewa Trump ya ce gwamnatinsa za ta nemi Iran ta biya diyya kan asarar da ya ce kasar ta haddasa wa Amurka cikin shekaru 50.
Ya ce:
"Sun nemi diyya, za ku iya cewa. Ko kuma sun nemi kuɗi kan barnar da muka yi. Na ce wannan kyakkyawan tunani ne."
Trump ya ƙara da cewa Amurka ma za ta nemi kuɗin barnar da Iran ta yi mata da sauran kasashe a cikin tsawon shekaru 50 da suka wuce.
'Dubban mutane sun mutu' Trump
Trump ya ce kuɗin diyya da yake nema za su shafi dakarun sojojin Amurka da aka kashe a yankin da kuma fararen hular da suka mutu a Iran.
Shugaban Amurka ya yi ikirarin cewa mutane 52,000 ne aka kashe a Iran cikin watanni huɗu da suka gabata.
Sai dai Tehran ta ce mutane kusan 3,117 ne suka mutu a zanga-zangar adawa da gwamnati da ta mamaye kasar a watan Janairub 2026.

Kara karanta wannan
Daga karshe Trump ya fadi kasar da za a dorawa alhakin kashe mutane a Gabas ta Tsakiya

Source: Getty Images
Wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam da ke Amurka ta bayar da wani adadi mafi girma, inda ta kiyasta cewa kusan mutane 7,000 ne suka mutu, ciki har da masu zanga-zanga 6,500.
Trump ya nemi diyyar USS Cole
Times of India ta wallafa cewa Trump ya ce ya kamata Iran ta biya iyalan sojojin ruwa 17 na Amurka da aka kashe a wani hari kan jirgin USS Cole a Yemen a watan Oktoban 2000.
Sai dai an daura alhakin harin USS Cole ne kan ƙungiyar al-Qaeda, ba Iran ba. Trump ya kuma ya kamata Iran ta ɗauki alhakin barnar da mutanen Lebanon, Syria, Yemen da Gaza suka fuskanta.
Trump ya yi tafiya a ɓoye
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya yi tafiya a cikin wani jirgin soji na sirri daga Turkiyya a watan da ya gabata, duk da cewa Fadar White House ta ce yana cikin jirgin Air Force One.
An ce matakin ya biyo bayan wata barazanar kashe Trump da Iran ta yi, yayin da shugaban ya halarci taron NATO a Ankara na Turkiyya.
Trump ya je taron ne da sabon jirgin da Qatar ta bai wa Amurka, amma lokacin barin Turkiyya ya yi amfani da wani tsohon jirgi, lamarin da ya haifar da tambayoyi kan tsaro da sabon jirgin.
Asali: Legit.ng

