Kasar Iran Ta Sake Kinkimo Rigima, Ta Kai Korafi gaban Majalisar Dinkin Duniya

Kasar Iran Ta Sake Kinkimo Rigima, Ta Kai Korafi gaban Majalisar Dinkin Duniya

  • Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai korafin Amurka ga Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar Kula da Harkokin Jiragen Ruwa ta Duniya
  • Iran ta shigar da wannan korafi a hukumance kan matakin da Amurka ta dauka na kwace mata wani jirgin ruwa
  • Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ke kara zafi tsakanin kasashen biyu, musamman kan batun mashigar ruwa ta Hormuz

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Iran ta shigar da kara a hukumance a gaban Majalisar Dinkin Duniya (UN) kan matakin da Amurka ta dauka na kwace wani jirgin kasuwanci mai dauke da tutar kasar.

Gwamnatin Iran ta kuma shigar da irin wannan korafi gaban Hukumar Kula da Harkokin Jiragen Ruwa ta Duniya domin a nema mata hakkinta kan Amurka.

Abbas Araghchi.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi yana jawabi a taron manema labarai a Tehran Hoto: Karim Jaafar
Source: Getty Images

Kasar Iran ta kai karar Amurka

Kara karanta wannan

Amurka ta farmaki jirgin Iran a teku, China ta fitar da gargadi ga Trump

Tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana lamarin a matsayin “haramtacce kuma rashin tausayi” daga bangaren Amurka.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar yau Talata, 21 ga watan Afrilu, 2026.

Ta ce an mika karar ga Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, da kuma Hukumar Kula da Harkokin Jiragen Ruwa ta Duniya, bayan da aka tare jirgin Touska a ranar Litinin.

Iran ta zargi Amurka da karya doka

Sanarwar ta nuna cewa matakin da Amurka ta dauka ya saba wa dokokin kasa da kasa, tare da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da ake kokarin aiwatarwa a halin yanzu.

“Jamhuriyar Musulunci ta Iran na gargadi kan hadarin da wannan haramtaccen aiki da na ta’addanci daga Amurka zai haifar.
"Muna kara jaddada bukatar sakin jirgin Iran nan take, da matukansa, ma’aikatansa da kuma iyalansu,” in ji sanarwar.

Har ila yau, Iran ta zargi cewa an yi amfani da barazana wajen aiwatar da wannan aiki, ciki har da tsoratar da ma’aikatan jirgin da iyalansu, in ji rahoton Middle East Eye.

Kara karanta wannan

An budewa jirgin Faransa wuta da zai wuce ta Hormuz da Iran ta toshe

Alakar Iran da Amurka na kara tsami

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da rikici tsakanin Tehran da Washington, musamman kan batutuwan tsaron hanyoyin ruwa da kuma matakan takaita zirga-zirga a yankin.

Masu lura da al’amura sun bayyana cewa irin wadannan matakai na iya kara dagula al’amura, tare da kawo cikas ga kokarin sulhu da ake yi tsakanin bangarorin biyu.

Guterres.
Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres yana jagorantar taro da wakilan kasashen duniya Hoto: Ludovic Marin
Source: Getty Images

Iran ta nanata cewa za ta ci gaba da kare muradunta a karkashin dokokin kasa da kasa, tare da daukar matakan da suka dace domin kare martabarta da ‘yancinta a fagen duniya.

Trump ya bukaci Iran ta dawo teburin sulhu

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa yana da ƙwarin gwiwar cewa Iran za ta amince ta shiga tattaunawa da Amurka duk da ta ɗan ja ƙafa.

Trump ya yi gargadin cewa idan hakan ba ta faru ba, ƙasar za ta fuskanci matsaloli masu tsanani fiye da duk abin da ta taɓa ganin irinsu ba a baya.

Ya ƙara da cewa yana fatan Iran za ta amince da yarjejeniyar da aka shimfida mai cike da adalci da za ta taimaka mata wajen farfaɗo da tattalin arzikinta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262