Iran na Ƙara Ɗaura Ɗamarar Yaƙi, Ta Ce ba za Ta Lamunci 'Zaluncin' Amurka ba
- Rundunar sojin Iran ta ce tana cikin cikakken shirin ko-ta-kwana, tana jiran duk wani hari daga dakarun Amurka
- Ta bayyana cewa za ta mayar da martani ta hanyar kai hari nan take kan wuraren da aka riga aka tsara idan aka kai mata hari
- Wannan na zuwa ne bayan kalaman Donald Trump kan tsawaita tsagaita wuta da kuma ci gaba da sa takunkumi a kan jiragen ruwan Iran
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Iran – Rundunar sojin Iran ta bayyana cewa tana cikin shirin ko-ta-kwana, inda ta ce za ta mayar da martani cikin gaggawa idan Amurka ta sake kai mata hari.
Iran ta fitar da sabon gargadin ne a safiyar ranar Laraba, 22 ga watan Afrilu na shekarar 2026 jim kaɗan bayan Donald Trump ya kara wa'adin tsagaita wuta.

Kara karanta wannan
"Abu 1 muke tsoro," Qatar ta tsoma baki kan batun tattaunawar sulhun Amurka da Iran

Source: Facebook
Al-Jazeera ta wallafa cewa M'mai magana da yawun rundunar, Ebrahim Zolfaghari, ya ce sojoji na cikin cikakken shiri domin tunkarar duk wata barazana.
Sojojin Iran na shirin sabon yaƙi
Anadolu Ajansi ta wallafa cewa a kalaman Ebrahim Zolfaghari, na za su zauna sakaka har Amurka ta sake kai masu wani harin zalunci ba.
A cewarsa:
"Rundunarmu mai ƙarfi da ƙwarewa ta dade tana cikin shiri 100%, kuma tana shirye, yatsa a kan bindiga."
Zolfaghari ya ƙara da cewa idan aka samu duk wani cin zarafi ko wuce gona da iri a kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, sojojin ƙasar za su kai farmaki cikin gaggawa da ƙarfi kan wuraren da aka riga aka sa wa ido.
Ya jaddada cewa matakan kariya da tsaro da Iran ke ɗauka ba sababbi ba ne, sai dai wani ɓangare ne na shirinta na kare kanta daga barazanar waje, musamman daga Amurka.
Gargaɗin Iran ya zo bayan kalaman Trump
Wannan sabon gargaɗi daga Iran ya biyo bayan kalaman shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya ce Amurka za ta tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran.
Trump ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne bayan wata buƙata daga jami’an kasae Pakistan, inda ya ƙara da cewa za a ci gaba da killace tashoshin jiragen ruwa na Iran.

Source: Getty Images
A cewarsa, ya umarci sojojin Amurka da su ci gaba da wannan aiki tare da tsawaita tsagaita wutar har sai Tehran ta gabatar da abin da ya kira tsari guda ɗaya a daftarin sulhu da ake don yi.
Matakin killace tashoshin jiragen ruwa na Iran na nufin hana zirga-zirgar jiragen ruwa na ƙasar, lamarin da ke da tasiri ga tattalin arzikinta da kuma hulɗarta da ƙasashen waje.
Trump ya magantu kan tsagaita wuta
A baya, mun wallafa cewa shugaba Donald Trump ya yi magana game da yakin Iran yayin da wa'adin tsagaita wuta da suka kulla zai kare a yau Laraba, 22 ga Afrilu, 2026.

Kara karanta wannan
Abin mamaki: Amurka ta taimaki kasar Musulunci ta Iran, ta yi abin alheri a Hormuz
Kalaman Trump sun nuna cewa ba za a cigaba da yakin ba duk da gaza cimma yarjejeniya da suka yi da Iran bayan zama da aka yi a.kasar Musulunci ta Pakistan.
Baya ga haka, kasar Iran ta kaucewa zama na biyu da aka so yi a Pakistan bayan an kai wa jirgin ruwanta hari, amma Amurka ta sanar da cewa JD Vance ya shirya tafiya kasar.
Asali: Legit.ng
