Trump Ya Fitar da Sanarwa yayin da Wa'adin Tsagaita Wuta da Iran zai Kare
- Shugaba Donald Trump ya yi magana game da yakin Iran yayin da wa'adin tsagaita wuta da suka kulla zai kare a yau Laraba, 22 ga Afrilu, 2026
- Kalaman Trump sun nuna cewa ba za a cigaba da yakin ba duk da gaza cimma yarjejeniya da suka yi da Iran bayan zama da aka yi a Pakistan
- Baya ga haka, kasar Iran ta kaucewa zama na biyu da aka so yi a Pakistan, inda Amurka ta sanar da cewa JD Vance ya shirya tafiya kasar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran, yana mai cewa sojojin Amurka za su dakatar da harin da suka shirya.
A baya, Trump ya sanar da cewa bai san halin da za a shiga ba idan wa'adin mako biyu da aka yi ya kare, inda ya ce da wahala ya tsawaita yarjejeniyar.

Kara karanta wannan
Kwana 1 kafin ci gaba da yaki, Shugaban Amurka ya fadi abin da yake tsammani daga Iran

Source: Facebook
Trump ya kara wa'adin tsagaita wuta
Matakin kara wa'adin tsagaita wuta da aka dauka a ranar Talata ya zo ne bisa bukatar masu shiga tsakani daga Pakistan, kamar yadda Trump ya yi ikirari a wani sako da White House ta wallafa a Facebook.
“Saboda haka na umarci sojojinmu su ci gaba da takunkumin toshe tashoshin ruwa, kuma a duk sauran bangarori su kasance cikin shiri, don haka zan tsawaita tsagaita wuta har sai sun gabatar da shawararsu kuma an kammala tattaunawa, ko ta yaya,”
In ji shugaban Amurka a wani sako.
Ba tare da ayyana takamaiman wa’adi ba, kalaman Trump na nuna cewa tsawaita tsagaita wutar na iya kasancewa ba tare da iyaka ba a bangaren Amurka.
Martanin Iran ga Donald Trump
Har yanzu Iran ba ta fitar da martani nan take ba kan kalaman Trump sai dai wani rahoto ya ce za a bayyana matsayar Tehran a hukumance daga baya.

Kara karanta wannan
"Babu lokaci," Trump ya sake maganar tashin hankali, ya mika zabin da ya rage ga Iran
Al Jazeera ta wallafa cewa Trump da farko ya ce bai goyi bayan tsawaita tsagaita wutar ba, yana gargadin Iran cewa lokaci na kurewa kafin Amurka ta kaddamar da babban hari.

Source: Getty Images
Sauya matsayar Trump ta zo ne yayin da jami’an Iran suka yi Allah-wadai da takunkumin ruwa da Amurka ta kakaba wa tashoshin jiragen ruwan kasar, lamarin da ya jefa shakku kan halartar su tattaunawar da za a yi.
Yakin Iran: Maganar kasar Pakistan
Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ya nuna godiya ga Trump bisa amincewa da tsawaita tsagaita wutar, yana mai cewa Islamabad za ta ci gaba da kokarin samar da mafita ta hanyar tattaunawa.
“Ina fatan bangarorin biyu za su ci gaba da mutunta tsagaita wuta kuma su cimma cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya a zagayen tattaunawa na biyu da za a yi a Islamabad domin kawo karshen rikicin gaba daya,”
In ji Sharif
An nemi EU ta rabu da Irsa'ila
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin kasar Spain na cigaba da matsin lamba domin ganin kungiyar tarayyar Turai (EU) ta raba hanya da Isra'ila.

Kara karanta wannan
Duk da kalaman Trump, Iran ta fito da gaskiyar abin ya kawo cikas a tattaunawa da Amurka
Spain na cigaba da caccakar Isra'ila ne saboda kisan kare dangi da Benjamin Netanyahu ya yi a Gaza da kuma kai hare-hare a Lebanon.
A wannan karon, Spain ta samu goyon bayan kasashen Slovenia da Ireland, inda suka hadu suka yi Allah wadai da hare-haren Isra'ila a Gaza.
Asali: Legit.ng