An Hango Matsala: An Hana Ƴar Siyasar Amurka da Ke Ƙin Jinin Musulunci Halartar Taro
- Gwamnatin Birtaniya ta hana wata ‘yar siyasar Amurka mai yada ra’ayin adawa da Musulunci shiga kasar
- Valentina Gomez ta shirya shiga kasar domin gangamin siyasa a London watan Mayun wannan shekara da muke ciki
- An shirya ta yi jawabi a taron 'Unite the Kingdom' da Tommy Robinson ke jagoranta, amma gwamnati ta ce akwak matsala shigarta kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
London, UK - An hana wata ‘yar gwagwarmaya daga Amurka mai suna Valentina Gomez shiga kasar Birtaniya.
Matakin ya biyo bayan ra’ayoyinta da ta ke yadawa masu tsattsauran ra’ayi na kin jinin Musulunci da al'ummar Musulmi.

Source: Facebook
Rahoton Sky News ta tabbatar da cewa an shirya gangamin ne a birnin London wanda za a gudanar a watan Mayun 2026.
Yaushe za a gudanar da gangamin a London?

Kara karanta wannan
"Abu 1 muke tsoro," Qatar ta tsoma baki kan batun tattaunawar sulhun Amurka da Iran
An shirya cewa Gomez za ta halarci taron Unite the Kingdom a ranar 16 ga Mayun 2026, wanda dan rajin siyasar masu tsattsaurar ra'ayi, Tommy Robinson ya shirya.
Rahotanni sun nuna cewa an amince da takardar shigarta ta ETA, amma daga baya gwamnati ta hana ta bayan matsin lamba daga ‘yan majalisa da masu fafutuka.
Gwamnati ta bayyana cewa shigarta ba ta dace da “amfanin jama’a” ba, irin dalilin da aka taba bayarwa wajen hana mawaki Kanye West shiga kasar.

Source: Twitter
Martanin Gomez kan hana ta shiga Birtaniya
Bayan an hana ta shiga, Gomez ta bayyana a shafukan sadarwa cewa za ta shiga Ingila ta ruwa, tana mai cewa ba za su iya dakatar da gaskiya ba.
A wani bidiyo da ta wallafa a X, ta zagi Ministar harkokin cikin gida, Shabana Mahmood tare da kalamai masu wariyar launin fata da kuma tsokana.
Gomez ta shahara wajen yada sakonni masu adawa da Musulunci a kafafen sada zumunta, har ma ta taba kona Al-Kur’ani a cikin wani bidiyo.
Dokokin Birtaniya na bai wa gwamnati damar hana ‘yan kasashen waje shiga idan hakan zai iya kawo barazana ga tsaro ko zaman lafiyar jama’a.

Kara karanta wannan
"Wasun su hotiho ne": Tsohon dan majalisa ya gargadi Tinubu kan dogaro da gwamnoni a 2027
Gwamnati ta jaddada cewa ‘yancin fadin albarkacin baki ba ya hada da yada kiyayya ko tsattsauran ra’ayi a cikin al’umma.
Kungiyar Muslim 'Council of Britain' ta yi maraba da matakin, tana cewa ya dace a hana masu yada kiyayya shiga kasar domin kare tsaro da hadin kai.
Ta bayyana cewa matakin ya tabbatar da cewa kasar na kare yancin gudanar da addini ba tare da nuna wariya da zai ci gaba da kawo gaba a tsakanin al'umma ba.
'Yar siyasa ta sha alwashin karar da Musulmai
Mun ba ku labarin cewa wata tsohuwar ‘yar takarar a jam'iyyar Republican, Valentina Gomez, ta tayar da hargitsi a taron Musulmi a Capitol na Texas.
Mutane da dama sun yi korafi tare da sukar matakin da yar siyasar ta ɗauka yayin taron da aka yi a kudancin Amurka.
Addinin Musulunci na cigaba da fuskantar kalubale a wasu kasashen duniya musamman a wasu yankunan Amurka wanda ke kara mata jawo fargaba kan yancin yin addini.
Asali: Legit.ng