Matawalle Ya Shiga Matsala, Ƴar Majalisar Amurka Ta Yi Gagarumin Zargi kan Minista
- Lambar Bello Matawalle ta fito bayan yar majalisar Kimberly Daniels ta zargi ministan da yunkurin ba da cin hanci
- Daniels ta yi wannan zargi ne game da neman sauya rahoton kisan Kiristoci a Nigeria da ake tuhumar Matawalle
- Ta ce an yi kokarin boye rahoton 'United World Congress of Diplomats' wanda ya zargi Matawalle da hannu a kashe-kashe a jihohin Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - ‘Yar majalisar Amurka daga Florida, Kimberly Daniels, ta zargi ƙaramin ministan tsaron Nigeria, Bello Matawalle, da kokarin bada cin hanci.
Daniels ta ce Matawalle ya yi yunkurin ba da cin hanci ne ga wani jami’in Amurka domin sauya rahoton 'United World Congress of Diplomats'.

Source: Original
Daniels ta bayyana haka ne a wani bidiyo da ya yadu wanda ta wallafa a shafinta na Facebook, inda ta ce an yi yunkurin rufe rahoton da ke zargin kisan Kiristoci a Nigeria.

Kara karanta wannan
An hango matsala: An hana ƴar siyasar Amurka da ke ƙin jinin Musulunci halartar taro
Daniels ta roki Tinubu ya sallami Matawalle
Wannan na zuwa ne bayan yar majalisar ta tsoma baki a cikin al'amarin tsaron Najeriya tare da ba Bola Tinubu shawara game da kujerar ƙaramin ministan tsaro a Najeriya, Bello Matawalle.
Wani rahoton tsaro da ta gabatar ya nuna karuwar hare-hare a lokacin bukukuwan Easter a jihohin Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma.
Daniels ta bukaci Bola Ahmed Tinubu ya duba shugabancin tsaro tare da ɗaukar mataki a kan Bello Matawalle wurin raba shi da kujerarsa.

Source: Facebook
Yar majalisar Amurka ta taso Matawalle a gaba
Ta ce babu wani matsin lamba da zai hana ta ci gaba da bayyana gaskiya, tana mai cewa an yi kokarin lalata rahoton tare da sayen goyon bayan ‘yan majalisa.
A cewarta, wani dan majalisar Amurka da ba a bayyana sunansa ba ya samu tayin kudi domin ya fito ya kare shugabannin tsaron Nigeria.
Daniels ta kuma ce tana da hujjojin sakonni da bayanai da aka shirya, wadanda ta alakanta da Bello Matawalle, domin sauya fahimtar jama’a kan rahoton.

Kara karanta wannan
"Abu 1 muke tsoro," Qatar ta tsoma baki kan batun tattaunawar sulhun Amurka da Iran
Ta kara da cewa wannan yunkuri na cin hanci na nufin raba kan ‘yan majalisar Amurka, ba tare da sanin cewa suna da hadin kai ba.
Ta tunatar cewa ta taba kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya kori Matawalle saboda zargin hannu a kashe-kashe a jihohi daban-daban.
Har yanzu dai Matawalle bai mayar da martani kan wadannan zarge-zarge daga ‘yar majalisar Amurka ba wanda ya kawo maganganu a tsakanin ƴan Najeriya.
Kamarawa ya magantu kan zargin Matawalle da ta'addanci
Mun ba ku labarin cewa tsohon hadimin Bello Matawalle ya sake bayyana kansa kan zargin alakar ministan da ta’addanci a bidiyon da ya tayar da kura.
A bidiyon da aka yada a shafukan sada zumunta, Kamarawa ya ce bai aikata wani abu da kansa ba a zamanin mulkin Bello Matawalle.
Musa Kamarawa ya rantse da Alƙur’ani Mai Girma, yana kalubalantar Matawalle da masu musun zargin da su rantse idan suna zarginsa.
Asali: Legit.ng