Amurka
Wasu daga cikin alkalan kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa (ICC) sun shigar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, kara a gaban kotu.
Dan majalisar Amurka, Riley Moore ya ce ya yi kokari a a bayyane da a sirrinace wajen ganin an kafa 'yan sandan jihohi a Najeriya. Ya ce ya yi maraba da dokar.
Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce Amurka ba ta bukaci Isra’ila ta janye sojojinta daga kudancin Lebanon ba yayin da ake maganar yarjejeniya da Iran.
Ministan tsaron Israila, Israel Katz, ya bayyana cewa ba za su janye dakarun sojojin kasar daga Kudancin Lebanon. Ya ce ko da Amurka ta bukata, ba za su yi ba.
Majalisar Dattawan Amurka ta amince da kudirin da ke neman hana Shugaba Donald Trump ci gaba da amfani da sojojin kasar wajen kai hare hare a Iran
Kasar Amurka ta sassauta takunkumin tafiye-tafiye da aka kakaba wa tawagar kwallon kafa ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran a gasar kofin duniya ta 2026 da ake yi.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce ƙasar ta kamata ta rage dogaro da makaman Amurka, tare da ƙarfafa masana’antun kera makamai na cikin gida domin tsaro.
Gwamnatin Donald Trump ta fadi sunayen mutanen da ake zargi da tallafawa ta'addanci wajen jigilar kudin ISIS a Najeriya. Ta ambaci wasu kamfanoi a Legas da Kano.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa za su sakin kudin Iran da aka rike amma za a yi amfani da wasu wajen sayen kayan abinci daga manoman Amurka.
Amurka
Samu kari