An Fitar da Hotunan Bindigogi da Wukaken da aka So Kashe Trump da Su
- Rahoto ya nuna cewa an gurfanar da wanda ake zargi da harbi a wajen taron ‘yan jarida bisa yunkurin kashe shugaba Donald Trump
- Alkalin da ya saurari shari'ar a ranar Litinin, 27 ga watan Afrilun 2026 ya karanta zarge-zargen da ake yi wa matashin sannan ya dage shari'ar
- Ma'aikatar shari'ar kasar Amurka ta wallafa hotunan makaman da aka samu wanda ake zargi da su da suka hada da bindigogi da wukake
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Hukumomin Amurka sun gurfanar da mutumin da ake zargi da harbin wani jami’in tsaro yayin da ya yi kokarin kutsawa wurin wani babban taron ‘yan jarida da Donald Trump ya halarta, bisa zargin yunkurin kashe shugaban kasar.
Wanda ake zargin, Cole Tomas Allen mai shekaru 31 daga Torrance, California, na kuma fuskantar tuhume-tuhumen mallakar makamai a cikin kara mai sassa uku.

Source: Getty Images
Rahoton da tashar Al Jazeera ta wallafa ya nuna cewa idan aka same shi da laifi, zai iya fuskantar hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.
Kashe Trump: An gurfanar da Allen
Allen ya bayyana a gaban kotun tarayya da ke Washington DC sanye da kayan gidan yari masu launin shudi, kwana biyu bayan jami’an tsaro suka ce sun dakile wani yunkurin kai hari a wajen liyafar kungiyar ‘yan jaridu ta White House.
“Ya yi yunkurin kashe shugaban Amurka, Donald J Trump,”
In ji mai gabatar da kara, Jocelyn Ballantine a kotu.
Allen bai mayar da martani kan zarge-zargen ba. Yayin da yake zaune a gaban lauyoyinsa tare da jami’an tsaro, ya ce zai amsa dukkan tambayoyi cikin gaskiya.

Source: Twitter
Alkalin kotun, Matthew Sharbaugh, ya bayar da umarnin ci gaba da tsare shi a gidan yari yayin da ake ci gaba da shari’ar, tare da sanya ranar Alhamis domin ci gaba da sauraron karar.

Kara karanta wannan
An kunyata 'yan jarida a zaman shari'ar wadanda ake zargi da kitsa juyin mulki a Najeriya
Maganar lauyar kasar Amurka
Babbar lauyar gwamnatin Amurka a Washington DC, Jeanine Pirro, ta ce ana iya kara wasu tuhume-tuhume a kansa yayin da bincike ke gudana.
“Ku sani sarai, wannan yunkurin kashe shugaban Amurka ne, kuma wanda ake zargin ya bayyana abin da yake son yi a fili – wato ya hallaka manyan jami’an gwamnati da dama gwargwadon ikonsa,”
In ji ta ga manema labarai a ranar Litinin.
Ta kuma ambaci wata takarda da ake zargin ya rubuta, inda aka nuna cewa ya tsara wadanda zai kai wa hari bisa matsayinsu daga manya zuwa kanana.
Makaman da zai kashe Trump da su
Pirro ta kara da cewa an gano yana dauke da bindiga mai sarrafa kanta, bindigar harba alburusai masu yawa da kuma wukake uku.

Source: Getty Images
Ma'akatar shari'ar Amurka ta wallafa hotunan makaman a shafinta, inda aka yi zargin cewa ya saye su ne a jihar California a kwanakin baya.
Trump ya sha kunya inji Merz
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz ya bayyana cewa shugaba Donald Trump da Amurka sun sha kunya a yaki da Iran.
Yayin da ya ke magana kan karfin Iran, Friedrich Merz ya ce shugabannin Tehran sun nuna karfin zuciya fire da yadda duniya ta yi zato.
Ya kuma kara da cewa Jamus na cigaba da nazari domin duba hanya mafi dacewa da za a bude mashigar Hormuz da Iran ta toshe bayan fara yakin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

