Masarautar Bauchi Ta ba Goodluck Jonathan Sarauta Mai Gwaɓi

Masarautar Bauchi Ta ba Goodluck Jonathan Sarauta Mai Gwaɓi

  • An ba tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, sarautar gargajiya ta Jigon Bauchi daga Masarautar Bauchi
  • Mai martaba Sarkin Bauchi, Rilwanu Adamu, ne ya naɗa Jonathan sarautar yayin wani biki da aka gudanar a fadar masarautar ranar Talata a Bauchi
  • Gwamna Bala Mohammed ya yaba wa masarautar kan karrama Jonathan, yayin da tsohon shugaban ya gode, tare da alkawarin mutunta dokoki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar..

Bauchi - Masarautar Bauchi ta ba tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, sarautar gargajiya na girma.

Masarautar ta ba Jonathan sarautar Jigon Bauchi saboda gudunmawarsa wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya, zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Jonathan ya samu babbar sarauta a masarautar Bauchi
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan. Hoto: Goodluck Jonathan.
Source: Twitter

An ba Jonathan sarauta a Bauchi

Mai martaba Sarkin Bauchi, Rilwanu Adamu, ne ya naɗa Jonathan sarautar a yayin wani biki da aka gudanar ranar Talata a fadar Sarkin da ke cikin garin Bauchi, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Dan takarar NDC: 'Abin da ya sa Najeriya ke bukatar Obi da Kwankwaso'

An karrama Jonathan ne saboda gudunmawar da ya bayar wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya, zaman lafiya da haɗin kan Najeriya.

Sarkin Bauchi ya bayyana Jonathan a matsayin shugaba nagari, inda ya yaba masa kan jajircewarsa wajen inganta zaman lafiya da dimokuraɗiyya a Najeriya.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, wanda ya jagoranci tawagar jami’an gwamnati da sauran manyan baki zuwa fadar Sarkin, ya gode wa masarautar.

Mohammed ya ce:

“Ba da wannan sarauta na nuna amincewa da gudunmawar Dakta Goodluck Jonathan wajen bunƙasa dimokuraɗiyya da haɗin kan ƙasa a Najeriya.”

Ya ƙara da cewa, shugabancin Jonathan da gudunmawar da ya bayar ga ƙasar sun cancanci a yaba musu tare da karrama shi.

An ba Jonathan sarauta a Bauchi
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan yayin karbar sarauta a Bauchi. Hoto: Bauchi Emirate Council.
Source: Facebook

Jawabin da Jonathan ya yi

A nasa jawabin, Jonathan ya gode wa Sarkin Bauchi da al’ummar jihar bisa wannan karramawa da aka yi masa, cewar Daily Post.

Jonathan ya ce:

Kara karanta wannan

Yadda za a sabunta fadar sarkin Gombe ta zama ta yi zarra a Arewa

“Na ji daɗin wannan karramawa sosai, kuma ina godiya ga Mai Martaba, Masarautar Bauchi da al’ummar Bauchi saboda wannan girma da aka yi mini.”

Ya yi alkawarin mutunta dokoki da al’adun Majalisar Masarautar Bauchi tare da kiyaye martabar da ke tattare da wannan sarauta ta gargajiya.

Jonathan ya ce:

“Zan ci gaba da mutunta al’adu da ƙa’idojin Masarautar Bauchi tare da tabbatar da cewa an kiyaye martabar da ke tattare da wannan sarauta.”

Majiyoyi ta ruwaito cewa tsohon shugaban ya isa Bauchi tun ranar Lahadi, yayin da a ranar Litinin ya ƙaddamar da wasu ayyukan tituna da gwamnatin Bala Mohammed ta gudanar.

INEC ta fitar da sunan yan takara

Kun ji cewa hukumar INEC ta fitar da jerin sunayen 'yan takarar zaɓen 2027 na ƙarshe, inda aka rasa sunan tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.

Fitattun sanatoci a Najeriya sun rasa sunayensu a cikin jerin takardun ƙarshe da INEC ta fitar wanda ke kara tabbatar da cewa sun damar tsayawa takara a 2027.

Duk da APC ta mayar da sanatoci shida bayan duba ƙorafe-ƙorafe, wasu fitattun 'yan siyasa sun ci gaba da kasancewa a wajen jerin sunayen ƙarshe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.