An Dawo Maganar Nukiliya, Amurka Ta Yi Gargadi Mai Tsauri ga Kasar Iran

An Dawo Maganar Nukiliya, Amurka Ta Yi Gargadi Mai Tsauri ga Kasar Iran

  • Ministan tsaron Amurka ya sake yin magana game da yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila wanda ke ci gaba da tayar da hankula
  • Pete Hegseth ya buƙaci Iran ta yi watsi da shirin mallakar makamin nukiliya cikin hanyar da za a iya tabbatarwa
  • Ya ce Amurka ba ta matsa neman yarjejeniya ba, yana gargadin cewa Iran na iya fuskantar rugujewar tattalin arzikinta sakamakon takunkumi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya yi magana game da maganar sulhu da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Hegseth ya bayyana cewa dole ne Iran ta yi watsi da duk wani yunƙuri na mallakar makamin nukiliya ta hanyar da za a iya tabbatar da ita.

Amurka ta sake gargadin Iran kan makamin nukiliya
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian da takwaransa na Amurka Donald Trump Hoto: Masoud Pezeshkian/Donald Trump.
Source: Getty Images

Gargadin Amurka ga Iran kan makamin nukiliya

Hegseth ya yi wannan jawabi ne yayin taron manema labarai a Pentagon, inda ya ce Iran na da muhimmiyar dama ta cimma yarjejeniya mai kyau, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Donald Trump ya dauki bindiga yana yi wa Iran sabuwar barazana

Ministan tsaron ya ce babu wata hanya ta samun sauki a maganar sulhu da ake yi illa kasar Iran ta yi wasti da maganar makamin nukiliya cikin lalama.

Ya ce:

“Abin da kawai ake buƙata daga gare su shi ne su yi watsi da makamin nukiliya ta hanya mai ma’ana kuma da za a iya tabbatarwa.”

Sai dai ya jaddada cewa Amurka ba ta cikin gaggawar cimma yarjejeniya da Tehran, yana mai cewa matsin lambar da ake yi wa Iran zai ci gaba idan ba ta sauya matsaya ba.

Amurka ta ja layi kan makamin nukiliyar kasar Iran
Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth yayin jawabi a Pentagon. Hoto: Alex Wong.
Source: Getty Images

Barazanar Amurka na maka wa Iran takunkumi

Hegseth ya yi gargadin cewa gwamnatin Iran na iya fuskantar rugujewar tattalin arzikinta ƙarƙashin matsin lambar Amurka da kuma killacewar da za ta ci gaba har sai an samu sauyi.

Ya ƙara da cewa:

“Ba ma ɗokin yarjejeniya. Iran na da zaɓi mai muhimmanci da za ta yi.”

Jami’in na Amurka ya kuma bayyana cewa dakarun ƙasar sun kama wasu jiragen ruwa biyu na Iran da ake kira “dark fleet” a yankin Indo-Pacific.

A cewarsa, jiragen sun yi tunanin sun tsere a kan lokaci amma hakan bai yiwu ba, yana mai cewa Amurka za ta ƙara kama wasu jiragen idan buƙatar hakan ta taso.

Kara karanta wannan

Da gaske jam'iyyar adawa ta yi wa Kwankwaso, Obi tayin takara? Gaskiya ta fito

Hegseth ya ce killacewar da ake yi wa Iran na ƙara faɗaɗa zuwa sassa daban-daban na duniya, inda ya bayyana cewa jirage 34 marasa alaƙa da Iran ne kawai aka bari su wuce.

Ya kuma gargadi Tehran cewa lokaci ba ya tare da ita yayin da matsin lamba ke ci gaba da ƙaruwa, kamar yadda shafin Iran International ya ruwaito.

Sakon Ministan tsaron Amurka ga Iran

Mun ba ku labari a baya cewa Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya gana da manema labarai a ranar Alhamis, 16 ga watan Afrilun 2026.

Pete Hegseth ya aika da sako ga shugabannin Iran yayin da ya bayyana cewa kasar ba ta da sauran karfin soja.

Ministan tsaron na Amurka, ya bayyana cewa Iran na kokari tono makamanta da aka birne a karkashin kasa sakamakon hare-haren da aka kai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.