Kasar Musulunci Ta Iran Ta Yi Sabon Zubi a Rundunar Sojojinta ana tsakiyar Yaki da Amurka
- Jagoran addinin Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei ya nada manyan kwamandojin soji shida domin inganta ayyukan rundunar kasar
- Ali Abdollahi ya zama Shugaban Hafsan Hafsoshin Sojojin Iran yayin da Ahmad Vahidi ya zama sabon kwamandan IRGC
- Haka zalika Khamenei na sa ran Mohsen Rezaee zai taka muhimmiyar rawa a tattaunawar Iran da kasashen waje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Islamic Republic of Iran - Jagoran Iran kuma kwamandan askarawan kasar, Mojtaba Hosseini Khamenei, ya sanar da nada manyan kwamandojin soji shida.
Kwamandojin za su aiki ne a wasu muhimman mukamai a rundunar sojin kasar, Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) da kuma rundunar Basij.

Source: Twitter
Tashar Al-Jazeera ta rahoto cewa Khamenei ya sanar da sababbin nade-naden ne ta shafinsa na Telegram.
Ya bayyana cewa ya rattaba hannu kan umarnin nada manyan jami’an soji a matsayin wani bangare na sauya tsarin jagoranci a bangaren tsaro na Iran.

Kara karanta wannan
Iran ta ƙara shiri, Mojtaba Khamenei ya yi wani muhimmin gyara ana cikin yaƙi da Amurka
Khamenei ya nada sababbin kwamandoji
Mojtaba ya nada Manjo Janar Ali Abdollahi a matsayin Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Iran, yayin da Birgediya Janar Kioumars Heydari ya zama mataimakinsa.
Haka kuma, Ahmad Vahidi, wanda aka daga masa matsayi zuwa Manjo Janar, ya zama sabon kwamandan Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran, wato IRGC.
An nada Mostafa Izadi a matsayin mataimakin Vahidi a shugabancin rundunar yayin da bangaren rundunar ruwa ta IRGC kuwa, aka nada Rear Admiral Ali Ozmaei a matsayin kwamanda.
Haka kuma, Hossein Taeb ya samu mukamin shugaban rundunar Basij, wata rundunar sa-kai mai matukar muhimmanci a tsarin tsaron Iran.
Sabbin nade-naden sun shafi wasu daga cikin manyan cibiyoyin tsaro da soji na Iran, lamarin da ke nuna yiwuwar samun sauyi a tsarin jagorancin bangaren tsaron kasar.
Rezaee na iya jagorantar tattaunawa
A wani bangaren, nadin Mohsen Rezaee a matsayin babban jami’in tsaron Iran na iya sauya salon da kasar ke bi wajen gudanar da tattaunawa da sauran kasashe.
Muhanad Seloom, mataimakin farfesa kan harkokin siyasar kasa da kasa da tsaro a Doha Institute for Graduate Studies, ya ce Rezaee na iya taka muhimmiyar rawa a duk wata tattaunawa da za a yi nan gaba.

Source: Getty Images
Ya bayyana cewa Rezaee tsohon kwamandan IRGC ne kuma mutum ne da Khamenei ya zaba da kansa, kamar yadda rahoton The Times of Israel ya nuna.
Seloom ya ce wasu raho tanni daga Iran na nuna cewa nadin Rezaee na iya kasancewa wani mataki na daidaita karuwar tasirin Kakakin Majalisar Iran kuma babban mai shiga tattaunawar kasar, Mohammad Bagher Ghalibaf.
Iran ta naɗa shugaban Majalisar tsaro
A wani labarin, kun ji cewa jagoran addini na kasar Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei ya nada Mohsen Rezaee da Mohammed Bagher Zolghadr manyan mukamai
Rezaee ya zama wakilin Mojtaba Khamenei a Majalisar Tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran a daidai lokacin da ake yaki da Amurka.
Rezaee ya jagoranci IRGC daga shekarar 1981 zuwa 1997, lokacin da rundunar ke kara karfafa matsayinta a tsarin tsaro da siyasar Iran.
Asali: Legit.ng
