Zargin Kisan Kiristoci: Amurka Za Ta Dauki Mummunan Mataki kan Kasar Najeriya

Zargin Kisan Kiristoci: Amurka Za Ta Dauki Mummunan Mataki kan Kasar Najeriya

  • Majalisar wakilan Amurka za ta sanya sharuɗa masu tsauri kafin a bai wa Najeriya tallafin tsaro, sakamakon kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci
  • Ɗan majalisar Amurka, Riley Moore, ya zargi gwamnatin Najeriya da kashe miliyoyin daloli a Washington maimakon magance matsalar tsaro a gida
  • Sharuɗan da Najeriya za ta fuskanta sun haɗa da kamo waɗanda ke da hannu a tashe-tashen hankula da kuma mayar da 'yan gudun hijira garuruwansu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka – Majalisar Wakilan Amurka tana ƙoƙarin ƙuntata tallafin tsaron da take bai wa Najeriya ta hanyar sanya wasu sharuɗɗa da dole sai gwamnatin tarayya ta cika su.

Wannan mataki ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da ɗan majalisa Riley Moore ya gabatar, inda ya zargi Gwamnatin Bola Tinubu da yin sakaci wajen kare mabiya addinin Kirista daga abin da ya kira "kisan ƙare dangi".

Kara karanta wannan

Bayan na Pantami, an tara wa dan majalisar tarayya miliyoyi domin takara

Dan majalisar Amurka, Riley Moore ya ce kasarsa za ta dauki mataki kan Najeriya game da kisan Kiristoci
Dan majalisar Amurka, Riley Moore da ya dage kan bin diddigin 'zargin kisan kiristoci' a Najeriya. Hoto: @RepRileyMoore
Source: Twitter

Amurka za ta dauki mataki kan Najeriya

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a daren Laraba, Moore ya bayyana cewa kwamitin kasafin kuɗi na majalisar ya riga ya amince da lissafin kuɗaɗen ma’aikatar harkokin wajen Amurka.

A cewarsa, wannan lissafin kuɗaɗen, yana ɗauke da matakan ladabtarwa ga Najeriya, ta fuskar tallafin tsaron da Amurka ta ke bai wa ƙasar.

"Gwamnatin Tinubu ta na kashe miliyoyin kudi wajen bin kafa a majalisa, yayin da ta gaza daukar matakan da suka dace don kawo karshen kisan kiyashin da ake yi wa Kiristoci a Najeriya.
"Majalisa ta amince da lissafin kuɗaɗen ma’aikatar harkokin waje, lamarin da zai dauki tsauraran matakai domin magance wannan matsalar"

— Riley Moore.

Sharuɗɗan da aka gindaya wa Najeriya

Moore ya bayyana cewa ya yi aiki tare da Mario Diaz-Balart domin tabbatar da cewa tallafin tsaron Amurka ba zai isa Najeriya ba muddin ba a tabbatar da abubuwa kamar haka ba:

Kara karanta wannan

Hormuz: Iran ta miƙa sabon tayin sulhu ga Amurka, an tabo batun makamin nukiliya

  • Daukar matakai masu tsauri kan tashe-tashen hankula da kuma gurfanar da mahara a gaban kotu.
  • Ba mutanen da suka rasa muhallansu fifiko wajen raba kayan tallafi.
  • Mayar da ƴan gudun hijira zuwa garuruwansu na asali.
  • Dole ne Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya tantance ko Najeriya ta cika waɗannan sharuɗɗan kafin a ba ta kowane irin tallafi.
Riley Moore ya zargin gwamnatin Najeriya da kashe miliyoyin daloli a toshiyar baki a Washington D.C.
Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang tare da Riley Moore a majalisar wakilan Amurka. Hoto: @CalebMutfwang
Source: Twitter

Tallafin Amurka ga tsaron jihohin Najeriya

Dokar ta kuma tanadi ware miliyoyin daloli na musamman domin magance tashe-tashen hankula a yankin tsakiyar Najeriya, musamman waɗanda ake zargin "Fulani makiyaya ne" suka aikata.

Baya ga haka, dokar tana ƙarfafa goyon bayan kafa rundunonin ƴan sandan jihohi a wurare irin su Filato da Binuwai, in ji rahoton Tribune.

Moore ya ƙara da cewa:

"Wannan matakin zai taimaka wa Kiristoci a Filato da Binuwai ta yadda ba za su zauna suna jiran tallafi daga Abuja ba yayin da ake farmakar su."

Sanatan Amurka ya tona asirin jami'an Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, Sanata Ted Cruz na Amurka ya zargi wasu manyan jami’an gwamnatin Najeriya da haɗa baki wajen kisan gilla ga Kiristoci a sassan ƙasar.

Ted Cruz ya ce daga 2009 zuwa yanzu, an kashe Kiristoci sama da 50,000 tare da ruguza majami'u da makarantu 20,000 saboda tsatsauran ra'ayi.

Amma a hannu daya, ma'aikatar wajen Amurka ta tabbatar da cewa Najeriya na nuna ƙoƙarin gyara wannan lamari ta hanyar ɗaukar matakai hudu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com