Shugaba Trump Bai Gamsu da Sababbin Sharuddan da Iran Ta Mika wa Amurka ba
- Shugaban Amurka, Donald Trump bai gamsu da sharuddan da ke kunshe a sabon tayin da kasar musulunci ta Iran ta gabatar masu ba
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kokarin sulhunta kasashen biyu domin kawo karshen yakin da ya shafe fiye da wata guda
- Sabon tayin na Iran ya bukaci a dakatar da tattaunawa kan shirinta na makamashin nukiliya har sai an kawo karshen yakin gaba daya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United states - Shugaban Amurka, Donald Trump bai gamsu da sabon tayin da Iran ta gabatar domin kawo karshen yakin fiye da wata guda da ya gudana a tsakanin kasashen ba.
Rahotanni daga fadar gwamnatin Amurka sun nuna cewa sabon tayin na Iran bai yi wa Trump dadi na, lamarin da ake ganin yana iya rage fatan samun maslaha cikin gaggawa.

Source: Getty Images
Abin da tayin Iran ya kunsa
Reuters ta tattaro cewa sabon tayin na Iran ya bukaci a dakatar da tattaunawa kan shirinta na makamashin nukiliya har sai an kawo karshen yakin gaba daya.
Haka zalika Iran ta bukaci a fara warware sabanin da ke akwai kan harkokin jigilar kaya a yankin Tekun Gulf.
Sai dai Amurka ta nuna cewa wannan tsari ba zai gamsar da ita ba, domin ta dage kan cewa dole ne a fara warware batun nukiliya tun daga farko.
Wani jami’in Amurka ya bayyana cewa rashin jin dadin Trump ya samo asali ne daga wannan matsaya ta Iran, bayan ganawar da shugaban ya yi da masu ba shi shawara a jiya Litinin.
Martanin Fadar White House
Mai magana da yawun fadar White House, Olivia Wales, ta ce Amurka ba za ta tattauna da Iran ta hanyar kafofin watsa labarai ba.
Ta kara da cewa gwamnatin Trump ta riga ta bayyana sharuddanta a fili yayin da take kokarin kawo karshen yakin da ta fara da Iran tun watan Fabrairu tare da hadin gwiwar Isra’ila.
Tarihin yarjejeniyar nukiliyar Iran
A shekarar 2015, an cimma wata yarjejeniya tsakanin Iran da wasu kasashe ciki har da Amurka, wadda ta takaita shirin nukiliyar Iran.
Sai dai yarjejeniyar ta rushe ne bayan Shugaba Trump ya janye Amurka daga cikinta a wa’adinsa na farko, kamar yadda tashar Al-Jazeera ta ruwaito.

Source: Getty Images
Kasar Iran dai ta dade tana cewa shirinta na nukiliya domin zaman lafiya ne kawai, bai shafi kera makaman yaki ba.
Wannan batu na shirin nukiliya shi ne babban abin da ke kara jawo tsaiko a tattaunawar sulhun Amurka da Iran, wacce aka fara a birnin Islamabad.
Trump zai kai hari da makamin nukiliya?
A wani labarin, kun ji cewa Donald Trump ya yi watsi da batun kai wa Iran hari da makamin nukiliya bayan barazanar da ya yi a baya na ruguza al'ummar kasar baki ɗaya.
Shugaban na Amurka ya bayyana cewa ba ya bukatar amfani da makamin nukiliya domin farmakar Iran da gamawa da ita.
Trump ya yi ikirarin cewa sojojin Amurka sun ruguza Iran ta hanyar amfani da makamai na yau da kullum ba tare da makamin nukiliya ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

