Amurka Ta Tafka Asara a Yaki da Kasar Musulunci ta Iran, Ta Kashe Kimanin Dala Biliyan 25
- Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ta kashe kimanin Dala biliyan 25 a yakin da kasar ta yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
- Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth ya tabbatar da cewa sun batar da makudan kudi wajen sayen makamai da kariya daga hare-hare
- Wannan na zuwa ne yayin da ake kokarin ci gaba da tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran bayan tsagaita wuta a yakin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Ma’aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) ta fito da wani rahoto da ke nuna makudan kudaden da ta kashe a yakin Iran, wanda ya shafe fiye da wata guda.
Ma'aikatar ta ce yaƙin da Amurka ta fafata da Iran ya lakume zunzurutun kuɗi kusan Dala biliyan 25, tun bayan barkewar rikicin a ƙarshen watan Fabrairun shekarar 2026.

Source: Getty Images
Amurka ta kashe Dala biliyan 25 a Iran
Wani babban jami’in ma’aikatar, Jules Hurst, ne ya tabbatar da hakan ga mambobin Majalisar Dokokin Amurka, kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
Ya ce mafi akasarin waɗannan kuɗaɗe an karkata su ne wajen gudanar da gagarumin aikin soja da aka yi wa laƙabi da “Operation Epic Fury."
A cewar Hurst, kuɗaɗen sun tafi ne wajen sayo manyan makamai, makaman kariya daga makamai masu linzami, da kuma tallafawa dakarun Amurka dake jibge a yankin Gabas ta Tsakiya.
Ministan tsaro ya kare Gwamnatin Donald Trump
To sai dai, Ministan Tsaro na Amurka, Pete Hegseth, ya yi ƙoƙarin rage fargabar jama’a game da yawan kuɗaɗen da kasar ta yi asara a yakin.
Ko da yake ya amince ana kashe kuɗi, Ministan ya yi ikirarin cewa adadin kudin da Amurka ta batar a yakin Iran bai kai Dala biliyan 25 ba, in ji rahoton Al-Jazeera.
Hegseth ya kare matakin gwamnatin Trump, inda ya bayyana cewa wannan aiki ne na "gaggawa" domin kare muradun Amurka.
"Tambayar da ya kamata kowane ɗan Amurka ya yi wa kansa ita ce, nawa ne darajar hana tsatson ta’addanci irin na Iran mallakar makamin nukiliya?" in ji Hegseth yayin da yake kare kasafin kuɗin yaƙin.
Rikicin ya samo asali ne tun ranar 28 ga watan Fabrairu, 2026, lokacin da dakarun Amurka da na Isra’ila suka ƙaddamar da jerin hare-hare kan cibiyoyin nukiliya da sansanonin sojin Iran.

Source: UGC
Yakin Iran na iya sauya siyasar Amurka
Wannan mataki ya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin wani yanayi na rashin tabbas wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a shekaru biyar ɗin nan.
Kodayake Shugaba Donald Trump ya sanar da ƙara wa’adin tsagaita wuta domin ba da damar tattaunawa, masana na ganin cewa hakan dabarar siyasa ce kawai.
Wannan yaƙi ya haifar da naƙasu ga tattalin arzikin duniya ta fannoni da dama, tun daga tashin farashin mai, tsadar rayuwa da matsi a harkokin kasuwanci.
A halin yanzu, idan ba a samu mafita ta dindindin ba, yaƙin Iran na iya zama babban sanadin canjin tsarin siyasar Amurka a zaɓe mai zuwa.
Amurka ta gargadi kasar Iran
A wani rahoton, kun ji cewa Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya bayyana cewa dole ne Iran ta yi watsi da duk wani yunƙuri na mallakar makamin nukiliya ta hanyar da za a iya tabbatar da ita.
Hegseth ya yi wannan jawabi ne yayin taron manema labarai a Pentagon, inda ya ce Iran na da muhimmiyar dama ta cimma yarjejeniya mai kyau.
Ya ce babu wata hanya ta samun sauki a maganar sulhu da ake yi illa kasar Iran ta yi watsi da maganar makamin nukiliya cikin lalama.
Asali: Legit.ng


