Majalisar Amurka Ta Yi wa Tinubu Gori, Ta Tsaurara ba wa Najeriya Taimakon Kudi
- ‘Yan majalisar Amurka sun amince da sababbin dokoki masu tsauri kan tallafin kuɗi ga Najeriya
- Za a riƙe kashi 50 cikin 100 na taimakon Amurka har sai an tabbatar da matakan dakile kashe-kashe a kasar
- Ƴan majalisar sun zargi gwamnatin Bola Tinubu da gaza kawo karshen zubar da jini duk da taimakon da aka ba ta
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
USA – Kwamitin kasafin kuɗi na majalisar wakilan Amurka ta amince da sababbin tanade-tanade da ke ƙara tsaurara kula da yadda ake ba Najeriya tallafin kuɗi daga ƙasashen waje.
Wannan ya fito ne a cikin kudirin kasafin kuɗin shekarar 2027 na ma’aikatar harkokin waje ta Amurka da kuma wasu shirye-shiryen tsaro da aka amince da su ranar Laraba.

Kara karanta wannan
Amurka ta tafka asara a yaki da kasar Musulunci ta Iran, ta kashe kimanin Dala biliyan 25

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta wallafa cewa ƴann majalisar sun danganta wannan mataki da zargin gazawar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen magance tashin hankali a ƙasarsa.
Majalisar Amurka ta fusata da gwamnatin Bola Tinubu
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa majalisar ta yi zargin akwai matsala da ke addabar Kiristoci, daga ciki har da hare-haren wasu ƙungiyoyi da ake dangantawa da Fulani da kuma ‘yan ta’adda amma Tinubu ya gaza magance su.
Kudirin ya tanadi jimillar kuɗi da suka shafi tsaro da yaƙi da ta’addanci da sauran shirye-shirye, sai dai bai ware takamaiman adadin da zai je Najeriya kai tsaye ba.

Source: Getty Images
Sabuwar dokar ta tanadi cewa kashi 50 cikin 100 na duk wani taimako da aka ware wa Najeriya ba za a fitar da shi ba sai Ministan harkokin waje na Amurka ya tabbatar cewa Gwamnatin Najeriya na ɗaukar matakai na dakile tashin hankali.
Haka kuma dole ne a tabbatar da cewa gwamnati na fifita tallafa wa waɗanda rikici ya shafa, musamman waɗanda suka rasa matsuguni a sassan Najeriya.
Abin da dokar Majalisar Amurka ta kunsa
Dokar ta kuma buƙaci gwamnati ta taimaka wajen tabbatar da komawar waɗanda aka raba da muhallansu gida cikin aminci, tare da sake gina yankunan da rikici ya shafa.
Majalisar Amurka ta nemi Najeriya ta bincika tare da hukunta duk masu hannu a hare-hare da ake zargi daga ƙungiyoyin makamai, tare da inganta tsaro ga fararen hula.
Haka kuma, kudirin ya tanadi cewa duk kuɗin Amurka da za a kashe a Najeriya dole ne a daidaita shi da irin gudummawar da Najeriya za ta bayar daga nata kasafin kuɗi.
Idan aka amince da dokar, Najeriya za ta shiga jerin ƙasashen da ke ƙarƙashin kulawa ta musamman, inda Amurka za ta rika sanar da Majalisar dokokinta kafin fitar da duk wani tallafi zuwa ƙasar.
Ana binciken harin Amurka a Najeriya
A baya, mun wallafa cewa Majalisar dokokin Amurka na neman cikakken bayani kan hare-haren sama da dakarun kasar suka kai Najeriya don yaƙar ƴan ta'adda.
A shekarar 2025 ne Amurka ta kai hari Sakkwato da aka ce da amincewar gwamnatin tarayyar Najeriya a ƙoƙarin da ake yi na hallaka ƴan ta'addan da suka addabi yankin.
'Yan majalisa na tambayar hujjar doka da ta ba shugaba Donald Trump damar tsallake su, da yaffa lamarin ya shafi fararen hula da gazawar makaman da aka harba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

