Khamenei Ya Fusata game da Barazanar Amurka, Ya Fadi Shirin Iran kan Makamin Nukiliya
- Jagoran addin a Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei ya yi magana game da shirinta na nukiliya a kasar
- Khamenei ya ce Iran ba za ta mika shirinta na nukiliya da makamai masu linzami ba, duk da matsin lambar Amurka
- Ya zargi Amurka da tsoma baki a yankin Gulf, yana mai cewa Iran za ta ci gaba da kare muradunta duk rikicin da ake ciki
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Jagoran addinin Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, ya yi martani ga barazanar Amurka kan makamin nukiliya.
Khamenei ya bayyana cewa kasar za ta kare shirinta na nukiliya da makamai masu linzami a matsayin kadarar kasa.

Source: Facebook
Jagoran ya yi wannan bayani ne yayin da Amurka ke neman sabuwar yarjejeniya bayan tsagaita wutar makonni uku da aka cimma a yakin, cewar rahoton Associated Press.
Musabbabin Iran na rufe mashigar Hormuz
A lokaci guda, Iran na ci gaba da rufe mashigar Hormuz, hanyar da ake jigilar kusan kashi daya cikin biyar na danyen mai na duniya.
Wannan mataki ya janyo tashin farashin gangar man Brent zuwa dala 126 a kasuwannin duniya.
Tsagaita wutar da aka cimma tsakanin bangarorin biyu na cikin mawuyacin hali, yayin da Amurka da Iran ke ci gaba da takun saka kan mashigar Hormuz.
Kasashen Gulf masu kawance da Amurka ma sun shiga damuwa saboda suna amfani da hanyar wajen fitar da makamashi.
Iran ta yanke shawara kan shirin nukiliya
Iran ta gabatar da shawarar dage tattaunawar shirinta na nukiliya zuwa gaba, Shugaba Donald Trump ya ce daya daga cikin dalilan da suka sa Amurka shiga yakin shi ne hana Iran mallakar makamin nukiliya.
Iran ta dade tana cewa shirinta na nukiliya domin zaman lafiya ne kawai, duk da cewa ta kara tace sinadarin uranium zuwa matakin kusan dacewa da kera makamin nukiliya.

Kara karanta wannan
Trump ya ki amince wa da wani bangare a sabon tayin sulhu da Iran ta yi wa Amurka
Pakistan ta ce har yanzu tana taimakawa wajen tattaunawar sirri tsakanin Iran da Amurka wanda ake ganin zai kawo karshen yakin da ake yi.

Source: Getty Images
Makamin nukiliya: Martanin Khamenei ga Amurka
Khamenei ya ci gaba da amfani da kalamai masu zafi tun bayan hawansa mulki bayan kashe mahaifinsa a hare-haren farko na yakin.
A cikin sanarwar da talabijin din gwamnati ya karanta, ya ce wurin da ya dace da Amurkawa a yankin Gulf shi ne karkashin ruwa.
Kalaman nasa sun zo ne yayin da rundunar sojin ruwan Amurka ke hana jiragen dakon man Iran fita teku, cewar The Guardian.
Wannan mataki yana hana Iran samun kudaden shiga daga man fetur, tare da kara matsin tattalin arziki ga kasar.
Jiragen yakin da Amurka ta yi asara
A baya, an ji cewa Gwamnatin Amurka ta yi asarar jiragen yaƙi da dama a rikicin da take yi da Iran wanda aka shafe fiye da wata guda ana yi.
Rahotanni sun nuna Iran ta harbo wasu jiragen F-15E, yayin da wasu suka faɗi sakamakon kuskure ko hatsari a wurare daban-daban ciki har da Gulf.
Hotuna da bayanai daga hukumomi sun tabbatar da lalacewar jirage irin su E-3 Sentry da kuma faduwar KC-135 da ya kashe mutane shida a Iraq.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
