Kasar Musulunci Ta Iran Ta Fara Rugujewa, Shugaban Amurka Ya Fadi Sakon da Aka Aiko Masa
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi ikirarin cewa Iran ta fara fuskantar rikici mai tsanani a tsakanin shugabanninta
- Ya ce sakamakon wannan rikici ne Iran ta roki Amurka ta taimaka wajen bude mashigar ruwa ta Hormuz domin ci gaba da hada-hada yadda ya kamata
- Wannan kalamai na Trump sun saba wa matsayar gwamnatin Iran, wacce ta sanar da rufe mashigar ruwan don maida martani ga Amurka
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United states - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ce Iran ta nemi a bude mashigar ruwa ta Hormuz domin ci gaba da hada-hadar jirage yadda ya kamata.
Trump ya yi ikirarin cewa kasar Musulunci ta Iran ta kama hanyar rushewa, don haka ta roki Amurka ta taimaka wajen bude mashigar ruwa ta Hormuz.

Source: Getty Images
Shugaba Trump fadi sakon kasar Iran
Tashar Al-Jazeera ta ce Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a wani sako da ya fitar yau Talata, 28 ga watan Afrilun 2025, inda ya ce Iran ta sanar da Amurka cewa tana cikin wani yanayi na “rugujewa.”
Ya ce Iran na son a bude mashigar Hormuz cikin gaggawa domin magance matsalolin shugabancin da take fama da shi.
"Yanzun nan Iran ta sanar da mu cewa ta kama hanyar rugujewa, sun nemi mu bude mashigar ruwa ta Hormuz kafin su shawo kan rikicin shugabancinsu, wanda nake da yakinin za su warware," in ji shi.
Muhimmancin mashigar Hormuz
Tun bayan fara yaƙin makonni tara da suka gabata, mashigar Hormuz wacce ke da matukar muhimmin ga tattalin arzikin duniya, ta zama makamim da Iran ke amfani da ita, inda ta rufe mashigar gaba daya.
Kusan kashi 20 cikin 100 na man fetur da iskar gas (LNG) na duniya na wucewa ta wannan hanya a lokutan zaman lafiya.
Rufe mashigar ya haifar da matsaloli a duniya, ciki har da fargabar durkushewar tattalin arziki da tsadar kayayyakin makamashi.
Rahotanni sun nuna cewa kusan jiragen ruwa 2,000 ne suka makale a yankin Gulf suna jiran izinin wucewa ta wannan mashiga.
Kalaman Trump sun saba da matsayar Iran
Sai dai bayan tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran, an fara tattaunawar sulhu domin warware sabanin da ke tsakanin kasashen da kuma bude mashigar ruwa ta Hormuz.
A farko, Iran ta bude mashigar domin cika sharuddan tsagaita wuta amma matakin da Amurka ta dauka na rufe tashohin jiragen ruwan Iran, ya sa ta sake rufe mashigar don maida martani.

Source: Getty Images
Yayin da ake ci gaba da wannna takaddama, Trump ya yi ikirarin cewa Iran ta roki Amurka ta bude mashaigar ruwa ta Hormuzsaboda rikicin da take fama da shi, in ji rahoton Fox News.
Wannan magana ta sabawa matsayar Iran, wacce ta sha nanata cewa ba za ta bude hanyar ruwam ba har dai Amurka ta bude tashohin ruwan fa ta rufe.
Trump bai gamsu da tayin Iran ba
A wani labarin, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump bai gamsu da sharuddan da ke.kunshe a sabon tayin da kasar musulunci ta Iran ta gabatar ba.
Sabon tayin na Iran ya bukaci a dakatar da tattaunawa kan shirinta na makamashin nukiliya har sai an kawo karshen yakin gaba daya.
Wannan batu na shirin nukiliya shi ne babban abin da ke kara jawo tsaiko a tattaunawar sulhun Amurka da Iran, wacce aka fara a birnin Islamabad.
Asali: Legit.ng


