Yadda Mahaifiyar Trump Ta Tsunduma a Kogin Son Sarkin Ingila Charles a Baya
- Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce mahaifiyarsa Mary Anne MacLeod Trump ta kasance mai matuƙar son gidan sarautar Birtaniya
- Trump ya ce mahaifiyar tasa na kallon duk wani bikin sarauniya a talabijin inda ya ce har nuna kauna take yi ga Sarki Charles a baya
- Shugaban Amurkan ya bayyana cewa mahaifiyarsa tana cewa Yarima Charles yana da kyau sosai tun yana matashi a wancan lokaci
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaba Donald Trump ya tarbi Sarki Charles da Sarauniya Camilla a Fadar White House inda ya yi jawabi kan dangantakar tarihi tsakanin Amurka da Birtaniya.
Trump ya bayyana cewa mahaifiyarsa Mary Anne MacLeod Trump, wacce aka haifa a Scotland, ta kasance mai tsananin son gidan sarautar Birtaniya tun shekaru masu yawa.

Source: Getty Images
Ya ce mahaifiyarsa tana bibiyar duk wani bikin sarauniya a talabijin, kuma tana nuna farin ciki sosai idan aka nuna wani abu game da sarauta, cewar rahoton People.
Yadda mahaifiyar Trump ta so Sarki Charles
Trump ya ce ya fada wa Sarki Charles cewa mahaifiyarsa tana yawan yabon shi lokacin yana ƙarami saboda kyawun fuskarsa da halayensa.
A yayin jawabin, Trump ya juya wajen kallon Sarki Charles sannan ya ce mahaifiyarsa tana da wata irin soyayya ga Charles tun yana saurayi.
Kalamin shugaban Amurkan ya sanya Sarki Charles dariya da sauran mutanen da suka halarci bikin tarbar 'yan gidan sarautar a White House.
Rahotanni sun bayyana cewa Trump da Sarki Charles na iya kasancewa ‘yan uwa na nesa ta silar wani tsohon ɗan sarautar Scotland mai suna John Stewart.
Majiyoyi suka ce an yi binciken danginsu ya nuna cewa suna da alaƙa ta jini daga zuriyar Earl na Lennox wanda ya rayu ƙarni da dama da suka gabata.
Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social cewa yana farin cikin wannan rahoto, yana mai barkwanci cewa yana son zama a fadar Buckingham wata rana.

Source: Getty Images
Jawabin Sarki Charles ga Donald Trump
A cikin ziyarar, Sarki Charles ya yi jawabi a gaban Majalisar Dokokin Amurka inda ya yi magana kan dangantaka da haɗin kai tsakanin ƙasashen biyu.
Sarkin ya tuna yadda ya kai ziyararsa ta farko Amurka a shekarar 1970, yana mai cewa ya daɗe yana mutunta jama’ar Amurka da tsarin dimokuraɗiyyarsu.
Ya kuma yi barkwanci cewa tsohon shugaban Amurka Richard Nixon ya taba ƙoƙarin haɗa shi aure da diyarsa Tricia lokacin da ya kai ziyara White House.
Wani dan Amurka mai amfani da X, Don Keith ya wallafa faifan bidiyo a shafinsa inda ya ce Trump ya yi kalamai cikin raha ga Sarki Charles.
Trump ya magantu kan sababbin sharudan Iran
A wani labarin, an ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump bai gamsu da sharuddan da ke kunshe a sabon tayin da kasar musulunci ta Iran ta gabatar masu ba.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kokarin sulhunta kasashen biyu domin kawo karshen yakin da ya shafe fiye da wata guda.
Sabon tayin na Iran ya bukaci a dakatar da tattaunawa kan shirinta na makamashin nukiliya har sai an kawo karshen yakin gaba daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

