Wata Sabuwa: Sheikh Jingir Ya Yi Karin Bayani kan Kalamansa da Suka Tayar da Kura a Najeriya
- Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi karin bayani kan kalaman da ya yi game da takarar musulmi da musulmi a wurin daura auren gata a Kano
- Shugaban Majalisar malamai ya ce kiransa na goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi a 2027 ra’ayinsa ne na kansa
- Ya ce ba matsayar kungiyar JIBWIS ba ce kuma bai kamata a dauke shi a matsayin umarnin kungiyar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Shugaban Majalisar Malaman Addini ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), reshen Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi karin haske kan kalamansa da suka jawo cece-kuce.
Sheikh Jingir ya nesanta kungiyar Izala daga kalaman da ya yi a baya na kira ga ’yan Najeriya su goyi bayan tikitin Musulmi da Musulmi a zaben shugaban kasa na 2027.

Source: Facebook
A wani rahoto da The Nation ta wallafa, Sheikh Jingir ya bayyana cewa matsayar da ya bayyana ta kasance ra’ayinsa ne kan halin siyasar Najeriya, ba matsayar kungiyar JIBWIS ba.
Malamin ya yi wannan karin bayani ne yau Talata yayin da yake magana da manema labarai a Kano, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun suka da muhawara kan kalaman da ya yi a baya.
Sheikh Jingir ya goyi bayan Tinubu
A baya, Sheikh Jingir ya yi kira ga musulmi da su goyi bayan Shugaba Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima a 2027 a karkashin tikitin musulmi da musulmi don su nuna su ke da ƙasa.
Kalaman sun jawo martani daga sassa daban-daban na Najeriya, musamman shugabannin lirista, kungiyoyin farar hula da masu sharhi kan harkokin siyasa.
Masu sukar kalaman sun yi gargadin cewa sake farfado da batun tikitin Musulmi da Musulmi na iya kara zurfafa rabuwar kawuna yayin da ake tunkarar zaben 2027.
Batun ya taba haifar da muhawara mai zafi a lokacin zaben 2023, lokacin da jam’iyyar APC ta tsayar da Tinubu da Shettima a matsayin dan takara da abokin takararsa dukkaninsu Musulmi.
Sheikh Jingir ya yi karin haske
Da yake bayani kan ce-ce-ku-cen da kalamansa suka haifar, Jingir ya jaddada cewa bai yi magana a madadin JIBWIS ba.
Ya ce:
“Kirana ga ’yan Najeriya da su goyi bayan Shugaba Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ba matsayar da kungiyar ta dauka ba ce. Ra’ayina ne na kaina.”
Sheikh Jingir ya kuma bukaci ’yan Najeriya su yi amfani da hakkokinsu na kundin tsarin mulki wajen zaben shugabanni a 2027.
Ya ce ya kamata masu kada kuri’a su yi nazari sosai kan ’yan takara da jam’iyyun siyasa kafin su yanke shawarar wanda za su goya wa baya.

Source: Twitter
Ya kuma yi kira ga shugabannin siyasa da na addini da su fifita zaman lafiya, hakuri da hadin kan kasa a lokacin da ake tunkarar babban zaben.
Malamin ya jaddada muhimmancin gudanar da abin da ya kira “siyasa cikin nauyi da sanin ya kamata”, domin kauce wa kalaman da za su iya kara rura rikicin siyasa ko na addini.
Tinubu ya ja hankalin musulmi da kiristoci
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya ce zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kiristoci na da matukar muhimmanci wajen ci gaban Najeriya baki daya.
Tinubu ya bayyana haka ne a yayin da gwamnatin tarayya da Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya za su gudanar da taron tsaro na ƙasa da ƙasa a Abuja
Asali: Legit.ng


