Shugaban APC Ya Tona Yadda Yan Siyasa ke Gwara Yan Najeriya da Sunan Addini

Shugaban APC Ya Tona Yadda Yan Siyasa ke Gwara Yan Najeriya da Sunan Addini

  • Shugaban APC, Nentawe Yilwatda, ya buƙaci malaman addini su riƙa faɗin gaskiya ba tare da tunzura ’yan Najeriya da neman haddasa fitina ba
  • Farfesa Yilwatda ya ce bambancin addini, ƙabila da al’adu ya kamata ya zama abin ado da alfahari ga Najeriya, ba abin da zai haddasa rikici ba
  • Ya ce siyasar da ake amfani da addini da ƙabilanci wajen samun moriyar siyasa na iya haifar da mummunar illa mai ɗorewa ga ƙasa baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja– Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya yi kira ga shugabannin addinai da su mayar da hankali wajen yaɗa zaman lafiya da sulhu, maimakon ƙiyayya da rarrabuwar kai.

Farfesa Yilwatda ya bayyana hakan ne ranar Talata11 ga watan Agusta, 2026 a Abuja, yayin wani taron ƙasa da ƙasa kan tsaron ƙasa da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yayyafa ruwan sanyi bayan kalaman Jingir sun ta da kura

Shugaban APC ya yi gargadi ga yan siyasa
Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda Hoto: Professor Nentawe Yilwatda
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta kawo labarin cewa kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS Nigeria) ce ta shirya taron tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Muslim World League ta ƙasar Saudiyya.

APC ta gargadi jagororin addini

Premium Times ta wallafa cewa Shugaban APC ya ce bambancin addinai, yare, al’adu da ƙabilu da ake da su a Najeriya ya kamata a ɗauke shi a matsayin ƙarfin ƙasa, ba abin da zai haifar da rikici da rashin fahimtar juna ba.

Yilwatda ya tuna lokacin da yake ƙarami, inda mahaifinsa, wanda fasto ne, ke da kyakkyawar alaƙa da babban limamin yankin da suke zaune.

Ya ce alaƙar shugabannin addinan biyu ta wuce bambancin addininsu, inda iyalansu ke yawan ziyartar juna tare da taya juna murnar bukukuwan addini.

Shugaban APC ya zargi yan siyasa da hada yan Najeriya rigima
Shugaban APC mai mulkin Najeriya Yilwatda Hoto; Professor Nentawe Yilwatda
Source: Facebook

Shugaban APC na kasa ya ce wannan mu'amala ta ƙarfafa imaninsa cewa bambancin addini bai kamata ya haifar da rarrabuwa tsakanin mutane ba.

Kara karanta wannan

NLC ta bude kofar tattaunawa da gwamnati, ma'aikata na iya samun karin albashi

Ya kuma bayyana cewa fahimtarsa game da illar rikicin addini da na al’umma ta ƙara zurfi bayan da aka tura mahaifinsa Bauchi a shekarar 1991 inda Musulmai da Kiristocu rika neman mafaka.

Shugaban APC ya yi magana kan siyasa

Shugaban APC ya ce shi ma ya zama ɗaya daga cikin waɗanda rikicin ya raba da muhallinsu, inda ya shafe kusan watanni uku a sansanin ‘yan gudun hijira.

Yilwatda ya ce Najeriya na fuskantar barazana da dama da suka haɗa da ta’addanci, ’yan bindiga, rikice-rikicen makamai, rikicin al’umma, ƙiyayyar ƙabilanci.

Sauran matsalolin da ya ambata sun hada da rashin jituwa tsakanin addinai, kalaman ƙiyayya da kuma amfani da bambancin ƙabila ko addini wajen cimma burin siyasa.

Ya yi Allah-wadai da ’yan siyasar da ke amfani da bambancin addini da ƙabila domin cimma muradunsu, yana mai cewa irin wannan dabara na iya kawo moriya na ɗan lokaci, amma ta bar babbar illa ga ƙasa.

Mungano dalilin Abba na komawa APC - NDC

A wani labarin kun ji cewa jam’iyyar NDC a jihar Kano ta mayar da martani ga kalaman hadimin gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature D-Tofa a kan jagoran Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Tinubu zai hallara a taron Izala da kungiyar Musulmin duniya za su yi

Jam’iyyar ta kuma nemi gwamnatin Kano ta fito da bayanai game da kuɗin da aka ce ta fitar domin gina wata makaranta, amma aka gano cewa babu ita ko alamarsu duk da an k ai ziyara yankin.

Mai magana da yawun jam’iyyar NDC a Kano, Hon. Yusuf Fasaha Majidadi, ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da Legit Hausa a jihar inda ya ce sun gano musabbanin Abba na rabuwa da Kwankwasiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng