Bidiyo: Sojoji Sun Yi Gumurzu da 'Yan Ta'adda a Daji, Sun Ceto Mutane
- Rundunar Sojin Najeriya ta jagoranci wani samame da ya kai ga ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su a jihar Kogi
- An ceto mutanen ne bayan haɗin gwiwar sojoji da rundunar sojin ruwa, 'yan sanda, 'yan banga da mafarauta a cikin daji
- Wani mafarauci ya rasa ransa yayin musayar wuta da masu garkuwa da mutanen, yayin da ɗan sanda guda ya samu raunuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Lokoja – Rundunar Sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro sun ceto mutane 16 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace a jihar Kogi.
An gudanar da aikin ceto ne bayan da jami'an tsaro suka samu bayanan sirri kan inda aka kai mutanen da aka sace.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da ceto mutanen ne a wani sako da rundunar sojin Najeriya ta walllafa a shafinta na X.
An yi garkuwa da mutane a Kogi
An sace mutanen ne ranar Lahadi, 9 ga Agusta 2026, lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hari kan matafiya a hanyoyin Ojuwo–Ajengo–Memarebo da Ojiwo–Itobe.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa hanyoyin suna cikin ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi.
Bayan samun sahihin bayanan sirri cewa an kai mutanen zuwa kusa da garin Adumu a ƙaramar hukumar Dekina, sojojin Bataliya ta 21 tare da jami'an NNS Lugard suka fara aikin ceto.
An yi musayar wuta da masu garkuwa
Sojojin sun gudanar da samamen ne tare da haɗin gwiwar 'yan sanda, 'yan banga da mafarautan yankin.
A yayin aikin, jami'an tsaron sun yi arba da masu garkuwa da mutanen, inda aka yi musayar wuta mai ƙarfi tsakanin bangarorin.

Kara karanta wannan
Nasara daga Allah: Sojoji da yan sanda sun rutsa yan bindiga fiye da 200 ta sama da ƙasa
Punch ta wallafa cewa jami'an tsaron sun rinjayi masu garkuwa da mutanen sakamakon ƙarfin makamansu da haɗin gwiwar da suka yi.
Masu garkuwar sun gudu zuwa cikin daji bayan sun bar dukkan mutanen da suka yi garkuwa da su, wasu daga cikinsu na fama da raunukan harbin bindiga.
An ceto mata, maza da yara
Jami'an tsaro sun samu nasarar ceto dukkan mutane 16 da aka yi garkuwa da su. Daga cikin wadanda aka ceto akwai maza shida, mata shida da yara huɗu.
A halin yanzu ana gudanar da bincike da rajistar bayanansu tare da duba lafiyarsu kafin a haɗa su da iyalansu kuma an kashe mafarauci, ɗan sanda ya samu rauni
Sai dai yayin aikin ceto mutanen, wani mafarauci da ya shiga aikin tare da jami'an tsaro ya rasa ransa.

Source: Facebook
Wani jami'in 'yan sanda shi ma ya samu raunuka yayin arangamar, kuma yana karɓar magani a asibiti. Rundunar ta yaba da jarumtar jami'an da mafarautan da suka shiga aikin domin ceto rayukan mutanen da aka sace.
Ga bidiyon da sojoji suka wallafa a kasa:
An kama dan bindiga a Enugu
A wani labarin, mun ruwaito cewa sojojin Bataliya ta 82 da ke ƙarƙashin Operation UDO KA, tare da jami'an DSS, sun kama wani da ake zargi da jagorantar ƙungiyar masu garkuwa da mutane a jihar Enugu.
An kama wanda ake zargin ne yayin wani samame da aka gudanar a yankin Gariki na jihar, inda sojojin suka kwato bindigogi AK-47 guda huɗu, magazin guda bakwai da harsasai 133.
Rundunar ta ce an gudanar da samamen ne domin tarwatsa wata ƙungiyar masu aikata laifuffuka da ake zargi da hannu wajen sace mutane biyu a ƙaramar hukumar Udi ranar 2 ga Agusta 2026.
Asali: Legit.ng

