Jirgin Rasha Ya Kutsa Cikin Ruwan da Amurka ta Jibge Sojoji Ta Hana Wucewa
- Ana cigaba da takun saka tsakanin Amurka da kasashen duniya bayan Donald Trump ya jibge sojoji a kusa da ruwan Hormuz domin hana wucewa
- Duk da matakn da Trump ya dauka, rahoto ya ce wani jirgin kasar Rasha ya wuce ta cikin tekun, kusa da sojojin Amurka ba tare da an tare shi ba
- Hakan na zuwa ne 'yan sa'o'i kadan bayan Firaministan kasar Rasha, Vladimir Putin ya gana da Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Wani katafaren jirgin alfarma mai alaka da daya daga cikin manyan abokan Firaministan Rasha, Vladimir Putin ya ratsa mashigar ruwa ta Hormuz, duk da takunkumin Amurka a kusa da wajen.
Jirgin ya yi tafiya daga Dubai zuwa Muscat na kasar Oman a karshen mako, kuma yana daga cikin ‘yan kadan daga jirage masu zaman kansu da suka ratsa mashigar a watannin baya-bayan nan.

Source: Getty Images
BBC ta wallafa cewa jirgin alfarmar mai suna Nord, wanda tsawonsa ya kai mita 142, ana alakanta shi da attajirin Rasha Alexey Mordashov da ke fuskantar takunkumi.
Jirgin Rasha ya wuce ta Hourmuz
Duk da yake Mordashov na da alaka ta kusa da Putin, ba a rubuta sunansa a matsayin mai jirgin a hukumance ba. Amma bayanan jirgin sun nuna cewa an yi masa rajista a karkashin wani kamfani mallakin matarsa a shekarar 2022.
Wani rahoton da Times of India ta wallafa ya nuna cewa ana kiyasta cewa darajar jirgin ruwan ta haura dala miliyan 500 a halin yanzu.
Jirgin ya bar Dubai a daren Juma’a, ya isa wata tashar jiragen ruwa mai suna Al Mouj a babban birnin Oman a safiyar Lahadi, kamar yadda bayanan hukumomi suka nuna.
Zirga-zirga a mashigar Hormuz
A halin yanzu, zirga-zirgar jiragen ruwa ta wannan mashigar ta ragu sosai idan aka kwatanta da yadda take kafin barkewar rikicin Amurka da Iran.

Kara karanta wannan
Mutanen jihar Kano na cikin alheri a mulkin Tinubu, an raba wa talakawa Naira biliyan 48
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya janyo tashin farashin mai a duniya, inda farashin danyen mai na Brent ya kai $109 a kowace ganga a ranar Litinin.
Iran na ci gaba da takaita zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa sojojin Amurka za su kakaba takunkumi kan tashoshin jiragen ruwa na Iran.

Source: Getty Images
Duk da haka, jirgin Nord mai dauke da tutar Rasha ya samu nasarar ratsa mashigar, yayin da yawancin jiragen masu zaman kansu ke kauce wa wucewa ta wurin tun bayan fara rikicin.
Iran ta tattauna da kasar Rasha
A wani rahoton, mun kawo muku cewa Vladimir Putin ya karbi bakuncin tawagar Iran a birnin St Petersburg a ranar Litinin, inda ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya jagorance su.
Putin ya shaida wa Araghchi cewa al’ummar Iran na fafatawa cikin jarumta wajen kare ikon kasarsu duk da matsin lambar Amurka da Isra’ila.
Araghchi ya bayyana cewa ziyarar da ya kai Rasha na da alaka da kokarin Iran na tattaunawa da kasashen duniya domin kawo zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
