Trump da Putin Sun Gana, An Tabo Yiwuwar Tsagaita Wuta a Ukraine

Trump da Putin Sun Gana, An Tabo Yiwuwar Tsagaita Wuta a Ukraine

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya tattauna da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin kan yiwuwar tsagaita wuta a Ukraine
  • Ya bayyana rashin tabbacin wane yaƙi zai fara ƙarewa tsakanin Ukraine da Iran wanda ke jawo matsaloli ga ƙasashen Turai
  • Kasar Rasha na iya sanar da tsagaita wuta a ranar bikin nasara da za a yi a 9 ga Mayu na shekarar 2027 mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Washington, USA — Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya yi wata doguwar tattaunawa da shugaban Rasha, Vladimir Putin.

Daga cikin batutuwan da suka mayar da hankali a kai har da yiwuwar ɗan gajeren tsagaita wuta a yaƙin Ukraine da ake gwabzawa har yanzu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya karyata jita jita, ya jero ayyukan da gwamnatinsa ke yi a yankin Arewa

Putin da Trump sun gana
Shugabannin Rasha da Amurka, Vladimir Putin da Donald Trump Hoto: Andrew Harnik
Source: Getty Images

CBS ta wallafa cewa Donald Trump ya faɗa wa manema labarai bayan kiran cewa ya ba Putin shawarar a samu ɗan sassauci a rikicin.

Trump da Putin sun gana kan Ukraine

Reuters ta wallafa cewa Trump ya ce yana ganin shugaban Rasha zai iya amincewa da wannan shawara ta tsagaita wuta a yaƙin da ƙasarsa ke yi da Ukraine.

Rahotanni daga Rasha, sun nuna cewa Putin ya ce yana shirye ya sanar da tsagaita wuta a ranar bikin Nasara ta Rasha, wanda ake yi a ranar 9 ga watan Mayu domin tunawa da nasarar da tarayyar Soviet ta samu kan Jamus a shekarar 1945.

Trump ya ce:

“Na ba da shawarar ɗan tsagaita wuta, kuma ina ganin zai iya yin hakan. Zai iya fitar da wata sanarwa dangane da hakan.”

Rahotanni sun ce tattaunawar tsakanin shugabannin biyu ta ɗauki fiye da mintuna 90, abin da ke nuna muhimmancin batun da suka tattauna.

Kara karanta wannan

Donald Trump: "Dalilin da ya sa ake yawan kawo mani hari"

Trump ya magantu kan yaƙe-yaƙe

A gefe guda kuma, Trump ya bayyana cewa ba shi da tabbacin wane yaƙi ne zai fara ƙarewa tsakanin rikicin Rasha da Ukraine da kuma rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran.

Shugaban Amurka ya ce bai san yakin da zai fara kare wa ba
Shugaban Amurka Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Twitter

Da yake amsa tambayar manema labarai, ya ce:

“Wane yaƙi ne zai fara ƙarewa? Ban sani ba. Wataƙila suna kan jadawali iri ɗaya.”

Trump ya nuna cewa yana ganin Putin na da sha’awar ganin an samu mafita ga rikicin Ukraine, yana mai cewa shugaban Rasha ya riga ya nuna shirin cimma yarjejeniya tun a baya.

Duk da haka, duk ƙoƙarin da Amurka ke yi na matsa lamba ga bangarorin biyu su cimma yarjejeniya bai kawo wani gagarumin ci gaba ba zuwa yanzu.

Shugaban Amurka ya ce yana fata cewa za a samu mafita cikin sauri, amma bai fayyace yadda ko yaushe hakan zai faru ba.

A yayin wannan tattaunawa kuma, Trump ya ce Putin ya bayar da shawarar taimakawa wajen batun sinadarin uranium na Iran, musamman dangane da rage ƙarfin sa.

Kara karanta wannan

Bayan boye boye saboda yaƙin Iran, Netanyahu ya fadi halin lafiyarsa

Sai dai Trump ya ce ya fi son shugaban Rasha ya mayar da hankali kan kawo ƙarshen yaƙin Ukraine, yana mai cewa wannan ne ya fi muhimmanci a halin yanzu.

Putin ya yi magana kan yakin Iran

A baya, mun wallafa cewa Firaminstan Rasha, Vladimir Putin ya yaba da jarumtakar jama'ar Iran yayin ziyarar ministan harkokin wajen Tehran, Abbas Araghchi.

Shugabannin kasashen biyu sun tattauna da juna ne yayin da ake ci gaba da samun takaddama tsakanin Iran da Amurka kan mashigar Hormuz yayin yakin Gabas ta Tsakiya.

Yayin ziyarar Firaministan Iran, Abbas Araghchi, Putin ya tabbatar masa da cewa suna kallon duk abin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya kuma suna tare da Iran a ko da yaushe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng