Ana Takaddama kan Makomar Sarkin Najeriya da Trump Ya Daure a Amurka
- Ana cigaba da takaddama kan makomar wani sarki a jihar Osun da aka daure a Amurka kan zamba bayan samun shi da laifi da aka yi
- Oba Joseph Oloyede ya shafe kusan shekara daya a garkame a Amurka, inda aka fara rade-radin cewa an sauke shi daga sarauta
- Sai dai gwamnatin jihar Osun ta fito ta yi karin bayani game da makomar Oba Joseph Oloyede yayin da ya ke cigaba da tsare a Amurka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Osun - An sake dawo da rade-radin cewa gwamnatin jihar Osun ta sauke Oba Joseph Oloyede da gwamnatin Donald Trump ta daure saboda zamba.
Yayin da ake cigaba da zargin cewa gwamnatin Osun ta sauke shi saboda tsare shi da aka yi, hukumomi sun yi karin bayani kan lamarin.

Source: Facebook
Gwamnatin Osun ta ce ba a sauke sarkin ba
The Nation ta rahoto cewa gwamnatin Jihar Osun ta karyata rade-radin cewa ta tube Apetumodu na Ipetumodu, Oba Joseph Oloyede, wanda aka samu da laifin zambar Dala miliyan 4.2 na tallafin COVID-19 a Amurka kuma aka yanke masa hukuncin dauri.
Idan ba a manta ba, an kama Oba Oloyededa ke da takardun zama dan kasa a Najeriya da Amurka ne a watan Mayu, 2024 yayin wata ziyara da ya kai kasar.
An cafke shi ne kan zargin damfarar kudin tallafin COVID-19 wanda daga bisani wani alkalin kotu a Amurka, Christopher Boyko, ya yanke masa hukuncin daurin wata 56.
Wata sanarwa da ba a tabbatar da ita ba ta bazu tana ikirarin cewa gwamnatin jihar Osun ta tube shi daga sarauta amma hukumomi sun karyata hakan.
Bayanin gwamnatin jihar Osun
Gwamnatin jihar Osun ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta da ke Osogbo, ta musanta batun tube Apetumodu na Ipetumodu.
Punch ta rahoto ya ce:
“Gwamnatin Jihar Osun ta lura da wata sanarwa ta karya da ke yawo.
"Ba daga Ma’aikatar Yada Labarai da Wayar da Kai ko kuma Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta ta fito ba. Ana shawartar jama’a, musamman ‘yan asalin Ipetumodu, da su yi watsi da wannan labari na karya.
“Gwamnatin jihar ta riga ta yi tattaunawa mai ma'ana da masu ruwa da tsaki na Ipetumodu, kuma ana daukar matakai bisa tsarin doka, wanda shi ne ginshikin tafiyar da wannan gwamnati.
“A lokacin da ya dace, za a sanar da jama’a da kuma ‘yan asalin Ipetumodu matakin da gwamnati za ta dauka ta hanyoyin sadarwa da suka dace.”

Source: Original
An daga shari'a kan sarautar Kano
A wani labarin, kun ji cewa kotu ta daga shari'ar da ake yi game da masarautar jihar Kano zuwa bayan babban zaben shekarar 2027.
Wanda ya shigar da kara, Aminu Babba Dan Agundi ya bayyana cewa daga shari'ar da aka yi zai ba su damar nazari sosai kan lamarin.
Dan Agundi ya bayyana cewa yana bukatar kotun ne ta rusa dokar da majalisar dokokin Kano ta kawo da ta dawo da Sanusi II.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

