Donald Trump Ya Dauki Bindiga Yana Yi wa Iran Sabuwar Barazana
- Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Iran barazana a wani sako da ya fitar da safiyar ranar Laraba yana dauke da bindiga sanye da tabarau
- Sakon na zuwa ne a lokacin da mashigar ruwa ta Hormuz ke ci gaba da kasancewa a rufe duk da tsagaita wuta da kasashen Amurka da Iran suka yi
- Haka zalika makomar tattaunawa da Iran na cikin rashin tabbas, bayan yunkurin ci gaba da zama a teburin sulhu a kwanakin baya ya tsaya cak
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi wata shiga da ta dauki hankali da da safiyar yau Laraba, 29 ga watan Afrilun shekarar 2026.
Rahotanni sun nuna cewa Donald Trump ya yi wa Iran barazana da bindiga yayin da har yanzu Tehran ba ta bude mashigar Hormuz ba.

Source: Facebook
Donald Trump ya yi gargadi da bindiga
Rahoton CNBC ya nuna cewa Donald Trump ya yi wa Iran barazana da makami ne a daidai lokacin da farashin makamashi ke kara tashi a duniya.
“Iran ba ta iya daidaita kanta. Ba ta san yadda za ta rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliya ba. Ya kamata ta fara hankali ba tare da bata lokaci ba!”
In ji Trump a sakonsa da ya wallafa da misalin karfe 4:00 na Asubahin ranar Laraba.
The Independent ta ce sakon ya zo tare da wani hoto da aka kirkira da fasahar AI, wanda ke nuna Trump rike da bindiga tare da abubuwan fashewa a bayansa, dauke da rubutun da ke nuna cewa:
“Babu maganar sassauci!”
Runadi kan zaman Amurka/Iran
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da mashigar Hormuz ke cigaba da kaancewa a rufe, yayin da tattaunawar da ake yi da Iran ke cikin rudani, inda kokarin ci gaba da zama ya gamu da tsaiko.
An shirya jami’an Amurka su je Islamabad na kasar Pakistan domin karin tattaunawa a karshen makon da ya gabata, amma Trump ya soke tafiyar.
“Dukkan karfi yana hannunmu,”
In ji shugaban a wata hira da ya yi yana mai cewa idan Iran na son tattaunawa:
“Za su iya zuwa gare mu ko kuma su kira mu.”
Tattaunawar da Mataimakin shugaban kasar Amurka, JD Vance ya jagoranta a baya ma ta kare ba tare da cimma matsaya ba a tsakanin kasashen.

Source: Facebook
A bangaren Tehran, ta bayar da shawarar cewa za ta bude mashigar Hormuz idan Amurka ta janye shingen da ta kakaba wa tashoshin jiragen ruwan Iran.
An gurfanar da mai son kashe Trump
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Amurka ta gurfanar da wani matashi da ake zargi da yunkurin kashe shugaban kasa Donald Trump.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan sanda samu matashin dauke da makamai da suka hada da bindigogi biyu da wukake masu kaifi guda uku.
Matashin ya bude wuta a wani wajen taro da Donald Trump da manyan jami'an gwamnatin Amurka ke ciki, inda ya tayar da hankalin kasar baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

