Iran Ta Gana da Rasha, Putin Ya Yi wa Tehran Alkawari kan Yaki da Amurka
- Firaminstan Rasha, Vladimir Putin ya yaba da jarumtakar jama'ar Iran yayin ziyarar ministan harkokin wajen Tehran, Abbas Araghchi
- Jagororin kasashen sun tattauna da juna ne yayain da ake cigaba da samun takaddama tsakanin Iran da Amurka kan mashigar Hormuz
- Abbas Araghchi ya bayyana cewa ya ziyarci kasar Rasha ne domin tattaunawa kan wasu muhimman abubuwa da suka shafi yaki da Amurka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Russuia - Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya je kasar Rasha domin ganawa da Vladimir Putin, wanda ya yaba da jarumtakar al’ummar Iran wajen kokarin kare ‘yancin kai da ikon kasarsu a yayin yaki da Amurka.
Da isarsa a ranar Litinin, Araghchi ya shaida wa kafafen yada labarai na Iran cewa ya je Rasha ne domin ci gaba da tuntubar juna kan batutuwan yankin da na duniya.

Source: Getty Images
Dalilin ganawar Iran da Rasha
Al Jazeera ta wallafa cewa Araghchi ya ce ganawarsa da Putin za ta ba da dama mai kyau don tattauna halin da ake ciki a yakin da kuma nazari kan sababbin abubuwan da ke faruwa.
Ya ce:
“Na yi imanin cewa irin wannan tuntuba da hadin kai tsakanin kasashen biyu na da matukar muhimmanci,”
Ziyarar na zuwa ne bayan wata ganawa da ya yi a Muscat da jami’an Oman, yayin da Iran ke kokarin samun goyon bayan kasashen yankin da na duniya.
Rawar da Rasha ke takawa
Wani rahoto daga Tehran ya nuna cewa ana sa ran Rasha za ta taka muhimmiyar rawa a mataki na gaba na wannan rikici da ake da Amurka.
“Akwai yiwuwar samun sulhu ta diflomasiyya, ko kuma a ci gaba da gwabzawa da juna,”
“Rasha za ta taka muhimmiyar rawa a dukkan bangarorin biyu, shi ya sa ministan harkokin wajen Iran ya je can domin tuntuba.”
In ji wani mai sharhi.

Source: Getty Images
Putin ya yi wa Iran alkawari
Yayin ziyarar Araghchi, Putin ya tabbatar masa da cewa suna kallon duk abin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya kuma suna tare da Iran a ko da yaushe.
“Mun ga yadda al’ummar Iran ke fafatawa cikin jarumta da kishin kasa domin kare ‘yancinsu da ikon kansu,”
In ji Putin, yana mai fatan za su shawo kan wannan mawuyacin hali kuma zaman lafiya ya samu.
“Mu kuma a bangarenmu, za mu yi duk abin da zai taimaka wajen kare muradunku da na al’ummar yankin gaba daya, domin a samu zaman lafiya cikin gaggawa,”
In ji shi.
Ga bidiyon bayanin Putin da Fox News ta wallafa a X:
Jamus ta caccaki Amurka
A wani labarin, kun ji cewa shugaban gwamnatin kasar Jamus, Friedrich Merz ya yi tsokaci kan yakin da Amurka/Isra'ila suka yi da Iran.
Friedrich Merz ya bayyana cewa Iran ta nuna jarumta sosai fiye da yadda aka yi zato wajen gwabzawa da dakarun Amurka/Isra'ila.
Ya kara da cewa Amurka ta sha kunya a yakin saboda rashin tsari, inda ya ce a yanzu haka Trump ya rasa hanyar fita daga rikicin.
Asali: Legit.ng

