Trump Ya Ki Amince wa da Wani Bangare a Sabon Tayin Sulhu da Iran Ta Yi wa Amurka
- Gwamnatin Amurka tana nazari kan wani sabon tayin zaman lafiya da Iran ta gabatar domin kawo karshen yakin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya
- Iran ta ce za ta bude mashigar Hormuz ga safarar jiragen ruwa, muddin Amurka za ta janye takunkumin soja da ta sanya wa tashoshin jiragen ruwan ta
- Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta nuna shakku kan wannan tayi, inda alamun farko ke nuna cewa Amurka ba za ta amince da shirin ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka – A daidai lokacin da duniya ke zuba ido kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka fara a ranar 8 ga watan Afrilu, 2026, kasar Iran ta gabatar da wani sabon tayin sullhu domin sassauta takun-saka a yankin Gulf.
Wannan shiri, wanda aka mika wa Washington ta hannun kasar Pakistan da ke matsayin karkon-zuma, ya mayar da hankali ne kan bude hanyoyin kasuwanci maimakon maganar makaman nukiliya da Amurka ke bukata.

Source: Getty Images
Sharadin Iran kan shirin nukiliya
Kasar Iran ta yi tayin bude mashigar ruwa na Hormuz, muddin Amurka za ta kawo karshen yakin tare da janye killace tashoshin jiragen ruwan Iran da ta yi, in ji rahoton Aljazeera.
Wannan killace tashoshin jiragen ruwa da Trump ya sanar kwanaki kadan bayan tsagaita bude wuta, ya nakasa tattalin arzikin Iran ta hanyar dakatar da fitar da danyen mai.
Babban abin da ya sanya Amurka shakku kan wannan tayi shi ne matsayar Iran na cewa dole ne a dakatar da tattaunawa kan shirinta na nukiliya har sai bayan an kawo karshen yaki baki daya.
Wannan yana nufin Iran ba ta shirya yin rangwame kan batun nukiliya ba domin kawai a bude mashigar Hormuz, lamarin da fadar White House ke ganin ba zai amfani muradun tsaron Amurka da Isra'ila na dogon lokaci ba.
Matsayar Amurka kan tayin Iran
A bangaren Washington, jami'an gwamnatin Trump sun nuna cewa wannan shiri ba zai samu karbuwa ba muddin babu takamaiman alkawari kan ruguza shirin nukiliyar Iran.
A cewar rahoton CNBC, wata majiya daga gwamnatin Amurka ta ce Trump bai ji dadin wannan tayi da Iran ta yi ba saboda bai kunshi batun nukiliyar Iran ba.
Majiyar da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida cewa "Trump ya ki amince wa da wannan tayi."
Wasu majiyoyi biyu daban sun bayyana cewa akwai yiwuwar Trump ya yi watsi da wannan tayi gaba daya, musamman ganin cewa Amurka na da wani abu da Iran take so.

Source: Getty Images
Abin da zai dawo da zaman lafiya a Gulf
Wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeid Iravani, ya jaddada matsayar kasarsa a ranar Litinin:
"Za a iya samun dauwamammen zaman lafiya da tsaro a Gulf da sauran yankuna ne kawai ta hanyar dakatar da duk wani nau'i na zalunci da cin zarafin Iran baki daya."
Masana na ganin cewa muddin ba a samu daidaito tsakanin bukatun Amurka na nukiliya da bukatun Iran na janye takunkumin tattalin arziki ba, yarjejeniyar tsagaita bude wutar da ake ciki za ta kasance mai rauni, wanda hakan na iya kai wa ga sake barkewar fada a kowane lokaci.
Trump ya yi magana kan Iran
A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaban Donald Trump ya yi ikirarin cewa Iran ta fara fuskantar rikici mai tsanani a tsakanin shugabanninta.
Ya ce sakamakon wannan rikici ne Iran ta roki Amurka ta taimaka wajen bude mashigar ruwa ta Hormuz domin ci gaba da hada-hada yadda ya kamata.
Wannan kalamai na Trump sun saba wa matsayar gwamnatin Iran, wacce ta sanar da rufe mashigar ruwan don maida martani ga Amurka.
Asali: Legit.ng


