Jihar Sokoto
Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal a ranar Juma’a, 10 ga watan Janairu ya yi umurnin fara biyan ma’aikata karancin albashi na 30,000 wanda aka aiwatar a jihar.
Rahoton da ke zuwa mana ya nuna cewa Allah ya yiwa dan Majalisar dokokin jihar Sokoto, Honarabul Isa Harisu Kebbe, rasuwa. Dan majalisar mai wakiltar karamar hukumar Kebbe ya rasu ne a yau Litinin, 30 ga watan Disamba.
Za ku ji yadda arangamar Bafarawa da Aliyu Wammako ta kaya a filin jirgi inda aka yi cacar-baki a gaban Jama’a tsakanin Sanata Wammako da Mai gidansa a baya.
Tattalin arzikin Najeriya ya dogara ne da kudaden shiga da gwamnati ke samu daga hada - hadar man fetur. Hakan yasa kasar ta dogara kacokan a kan tattalin arzikin man fetur tare da wofantar da sauran albarkatun da kasa keda su.
Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa a kasuwannin dabbobin jahar Sakkwato ana iya samun akuya maimatsakaicin girma a kan karamin kudi kamar N4,000, wanda hakan ke nuna rashin damuwa da akuya da jama’an yankin suke yi.
Siyar da wiwi a jinina yake- Wannan ne kalaman da suka fito daga bakin wani mutum mai suna Umaru Shehu, wanda jami’an yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyi suka cafke. Sun kama Umaru Shehu ne yayin da yake safarar ganyen wiwi...
Za ku ga jerin Jihohin Najeriya da Gwamnonin-baya ke karbar fansho duk wata. A Adamawa, Benuwai, Enugu, Kebbi, Kogi, Nasarawa, Ogun, Filato da Taraba, ne kurum ba a bada wannan kudi.
Majalisar dattawa a ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamba, ta rantsar da Sanata Abdullahi Danbaba mai wakiltan Sokoto ta Kudu. Danbaba na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya maye gurbin Shehu Tambuwal daga APC.
Kotun daukaka kara, da ke zama a Sokoto ta tabbatar da Sanata Ibrahim Danbaba Dambuwa da Dr. Balarabe Shehu Kakale na jam’iyyar Peoples Democratic Party a matsayin wadanda suka lashe zaben majalisar dokokin tarayya a yankin Sokoto
Jihar Sokoto
Samu kari