Hajjin bana: Gwamna Tambuwal ya yi umurnin mayarwa da maniyyata kudinsu

Hajjin bana: Gwamna Tambuwal ya yi umurnin mayarwa da maniyyata kudinsu

- Gwamnatin jihar Sokoto ta umurci hukumar jin dadin alhazai ta jihar da ta maida wa wadanda suka biya kudin aikin hajjin 2020 a jihar kudinsu

- Hakan ya biyo bayan soke aikin hajjin bana da kasar Saudiyya ta yi saboda annobar Coronavirus

- Dange ya bayyana cewa za a biya wadanda suka bukaci a dawo masu da kudadensu daidai da tsarin NAHCOM

- Ya shawarci maniyyatan da su karbi wannan lamarin a matsayin kudirin Allah madaukakin sarki

Gwanna Aminu Waziri Tambuwal ya umurci hukumar jin dadin alhazai ta jihar Sokoto da ta maida wa wadanda suka biya kudin aikin hajjin 2020 a jihar kudinsu.

Hakan ya biyo bayan soke aikin hajjin bana da kasar Saudiyya ta yi saboda annobar korona.

Da yake magana da jaridar Daily Trust ta wayar tarho, Darakta Janar na hukumar, Shehu Muhammad Dange ya ce gwamnan ya umurcesu da su fara shirin mayar da kudaden da maniyyatan suka tattare.

Hajjin bana: Gwamna Tambuwal ya yi umurnin mayarwa da maniyyata kudinsu
Hajjin bana: Gwamna Tambuwal ya yi umurnin mayarwa da maniyyata kudinsu Hoto: The Guardian
Asali: UGC

“Mun umurci jami’an aikin hajji na kananan hukumomi da su tattara takardun bayanansu sannan su gabatarwa da hukumar don tantancewa domin kada a samu kowani matsala” in ji shi.

Hukumar kula da jin dadin alhazai ta kasa ta bai wa jihar kujeru 4,500 kafin a soke aikin hajjin.

Dange ya bayyana cewa za a biya wadanda suka bukaci a dawo masu da kudadensu daidai da tsarin NAHCOM.

KU KARANTA KUMA: Kudin wuta: Shugabannin majalisa sun hadu da Buhari don saukakawa talakawa

“Amma kila akwai wadanda za su so a ajiye kudin saboda hajjin 2021,” in ji shi.

Ya shawarci maniyyatan da su karbi wannan lamarin a matsayin kudirin Allah madaukakin sarki.

A wani labarin kuma, Gwamna Aminu Tambuwal, ya musanta rahoton hukumar kididdiga ta kasa na cewa jiharsa na daya daga cikin jihohin da suka fi kowanne talauci a kasar nan.

Tambuwal ya yi wannan maganar ne bayan rahoton da ya samu mai taken "Tsarin habaka Sokoto: 2020-2025 a gidan gwamnatin jihar."

Kamar yadda NBS ta fitar da rahoton a watan Afirilun 2020, ta ce jihar Sokoto ce ta 9 a jerin jihohi 10 da talauci ya samu wurin zama a Najeriya daga yankin arewa. Sokoto, Taraba da Jigawa ne ke kan gaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng