Zamfara, Katsina da Sokoto: Dakarun soji sun ragargaza 'yan bindiga

Zamfara, Katsina da Sokoto: Dakarun soji sun ragargaza 'yan bindiga

Sakamakon ci gaban ayyukan dakarun sojin Najeriya na ganin tabbatar zaman lafiya a arewa, rundunar Operation Hadarin Daji karkashin Operation Accord ta ci gaba da samun nasarori wurin yaki da 'yan ta'adda.

Kamar yadda shugaban fannin yada labarai na runduna sojin, John Enenche ya bayyana, a ranar 26 ga watan Yuni, an dakile wani harin 'yan ta'adda a Mara Zamfarawa da ke karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.

A wannan halin dakarun suka halaka 'yan bindiga shida yayin da sauran suka tsere da raunina munana na bindiga.

Hakazalika, a ranar 27 ga watan Yunin, biyo bayan wani sintirin da dakarun suka yi bayan samun rahoton sirri a kauyen Dunya a karamar hukumar Danmusa, sun yi nasarar damke wasu wadanda ake zargin suna kaiwa 'yan bindiga bayanai. A halin yanzu ana tuhumar su don karin bayani.

A wani cigaba mai alaka da hakan, dakarun sun kai samame a kauyukan Mara Zamfarawa da Birchi Malamawa na karamar hukumar Danmusa. 'Yan bindigar sun tsere da miyagun raunika. Dakarun sun samo babura 4.

Duk da haka sun garzaya garin Maidabino inda suka kama 'yan bindiga 6 tare da samun bindiga kirar AK 47 daya, harsasai 29, adduna da layu.

Zamfara, Katsina da Sokoto: Dakarun soji sun ragargaza 'yan bindiga
Zamfara, Katsina da Sokoto: Dakarun soji sun ragargaza 'yan bindiga Hoto: Hedkwatar tsaro
Asali: Twitter

A wani ci gaba na daban, a ranar 27 ga watan Yunin 2020, bayan bayanan sirrin da dakarun suka samu, jami'an tsaro sun isa dajin Kurubka. Sun kashe 'yan bindiga biyu yayin musayar wuta da aka yi tsakaninsu da jam'ina tsaro.

A jihar Zamfara, bayan rahoton sirrin da dakarun suka samu a ranar 27 ga watan Yuni, sun tarwatsa maboyar 'yan bindigar da ke dajin Rambadawa, kilomita kadan kafin kauyen Kodamyo da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Zamafa.

Sun halaka 'yan bindiga uku tare da raunata wasu masu tarin yawa. Sun samo wasu bindigogi.

Har ila yau, a ranar 27 ga watan Yunin, sojojin sun kai samame kauyukan 'Yar Galadima da Mashanyin Zaki da ke Dansadau. Sun kashe 'yan bindigar da ke kan babura hudu sannan sun yi nasarar ceto mutum biyu da aka yi garzkuwa dasu.

Sun samo wata mota kirar Volkswagen mai lambar rijista MRR 47 XA. Dakarun sun zauna a yankin don samun ceton sauran wadanda aka yi garkuwa dasu.

KU KARANTA KUMA: Ina matukar farin ciki da rikicin APC - Gwamna Wike

A tsaunikan Gummi da garin Tambuwal da ke jihar Sokoto, dakarun sun kashe dan bindiga daya tare da samo bindigogi 5, adduna, wiwi da dubu sittin.

Rundunar sojin Najeriya na taya dakarun murnar wannan nasarorin da suka samu tare da basu kwarin guiwar bayyana kwarewarsu don shawo kan matsalar tsaron da ta addabi kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel