Rundunar sojin sama ta kaddamar da wani sabon aiki na ragargazar 'yan daban daji a Sakkwato

Rundunar sojin sama ta kaddamar da wani sabon aiki na ragargazar 'yan daban daji a Sakkwato

Rundunar sojin saman Najeriya ta kaddamar da wani sabon aiki na ragargazar ‘yan bindiga a jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Wannan ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan bindiga da dama da kuma lalata wasu daga cikin sansanoninsu.

Dakarun Operation Hadarin Daji ne suka aiwatar da wannan aiki mai cike da nasara.

A wani jawabi daga kakakin rundunar sojin sama, Air Commodore Ibikunle Daramola, a ranar Talata, ya ce an aiwatar da aikin ne a ranar 6 ga watan Yuli, Channels TV ta ruwaito.

A cewarsa, shirin rundunar sojin na kakkabe yan fashi, barayin shanu, masu garkuwa da mutane da sauran miyagu daga yankin na da hadin gwiwar hedkwatar tsaro karkashin Operation Accord.

Rundunar sojin sama ta kaddamar da wani sabon aiki na ragargazar 'yan daban daji a Sakkwato
Rundunar sojin sama ta kaddamar da wani sabon aiki na ragargazar 'yan daban daji a Sakkwato Hoto: Channels TV
Asali: UGC

A halin da ake ciki, shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar, ya jadadda jajircewarsa wajen yaki da miyagu a jihohin arewa maso yamma.

Abubakar wanda ya kasance a Sakkwato don shugabantar tsare-tsare da kaddamar da aikin, ya nuna jin dadi a kan nasarar da aka samu zuwa yanzu.

Ya bayyana cewa yayinda ake ci gaba da aikin ragargazar, rundunar sojin saman na aiki tare da sauran dakarun sojin kasa domin tabbatar da cewar an gama da yan bindigan da suka tsere ma harin saman ta kasa.

KU KARANTA KUMA: Manyan jami’an yan sanda sun fara kamun kafa domin maye gurbin Ibrahim Magu a EFCC

Shugaban sojin saman ya bayyana cewa saboda dajin Kagara ya kai har jumhuriyyar Nijar, akwai wata yarjejeniya da ake kullawa da hukumomin kasar.

Hakan ya kasance ne don tabbatar da cewar yan bindigan basu tsere ba ta iyakokin kasashen waje.

Yayinda yake kira ga goyon bayan dukkanin yan Najeriya, ya ba mutane tabbacin kokarin da rundunar soji ke yi na samar da kwanciyar hankali da muhalli mai cike da tsaro.

A wani labari na daban, jami’an yan sanda sun kama wasu da ake zargin matsafa ne kan yawan kashe-kashen bayin Allah da ake yi a yankin Akinyele, Ibadan.

Hadimin Gwamna Seyi Makinde na musamman a kan tsaro, Mista Fatai Owoseni ne ya bayyana hakan yayinda yake jawabi a wani taro a Akinyele a ranar Laraba.

Gidan radiyo mai zaman kansa na JAMZ 100.1 FM ne ya shirya taron.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel