ICPC ta bankado badakalar miliyan N250 a asibitin UDUTH da ke Sokoto

ICPC ta bankado badakalar miliyan N250 a asibitin UDUTH da ke Sokoto

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin ma'aikata da masu rike da mukaman gwamnati (ICPC) ta ce ta bankado badakalar miliyan N250 a asibitin koyarwa na jami'ar Usamanu Danfodio (UDUTH) da ke Sokoto.

Kakakin hukumar, Rasheedat Okoduwa, ce ta sanar da hakan a cikin wani jawabi da ta fitar ranar Talata a Abuja.

ICPC, ta bakin Rasheedat, ta yi zargin cewa an karkatar da kudaden daga asusun asibitin zuwa wasu asusu mallakar "wani mutum da wani kamfani".

Sai dai, hukumar ICPC ba ta bayyana sunayen mutanen da ake zargin sun mallaki asusun da aka karkatar da kudaden ba.

A cewar Rasheeedat, tuni hukumar ICPC ta kama wani ma'aikaci a bangaren kudi wanda shi ake zargi da zama kanwa uwar hadi a karkatar da kudaden.

"Ya na amsa tambayoyi da zasu kai ga gano sauran wandanda suke da hannu a cikin badakalar.

"ICPC ta fara kokarin kwace duk wasu kadarori da suka hada da gidaje da motocin alfarma daga hannun ma'aikacin da aka kama da sauran wadanda ake sa ran za a kama nan gaba," a cewarta.

ICPC ta bankado badakalar miliyan N250 a asibitin UDUTH da ke Sokoto
Asibitin UDUTH da ke Sokoto
Asali: Twitter

Kazalika, a wani labarin da Legit.ng ta wallafa, rundunar 'yan sanda ta kama wani mutum, Mallam Aminu Ado, mai shekaru 58, wanda ke sojan gona ta hanyar gabatar da kansa a matsayin matar marigayi Abba Kyari domin ya damfari jama'a.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kubutar da ma'aikata 600 da aka rufesu tsawon wata 3 a wani kamfanin shinkafa a Kano

Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, DCP Frank Mba, ya gabatar da mai laifin a gaban manema labarai a ranar Litinin.

Mba ya bayyana cewa an fi sanin mutumin da 'Al Amin Yerima', kuma da ma tsohon mai laifi ne da ya kware wajen shirya salo salon damfara.

A cewar Mba, Yerima ya na tuntubar manyan mutane a wayar salula da sunan matar marigayi Abba Kyari tare da neman tallafi da gudunmawa domin shiryawa marigayin addu'o'i na musamman.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng