'Kayar da Tinubu Ya Fi Komai Sauki,' Hakeem Baba Ahmed Ya Karfafi 'Yan Adawa
- Shugaban jam'iyyar PRP na ƙasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasar da ya fi sauƙin kayarwa a zaɓen 2027
- Hakeem Baba-Ahmed ya ce idan aka gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci, shugaba Bola Tinubu zai sha kaye a jihohi da dama a Najeriya
- Ya kuma zargi wasu mutanen da ke kewaye da shugaban ƙasar da ba shi bayanan ƙarya kan damar da yake da ita ta sake lashe zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban jam'iyyar PRP na ƙasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban ƙasar da ya fi sauƙin kayarwa a zaɓen 2027.
Ya ce yana ganin Tinubu na kewaye da mutanen da ke ba shi shawarwari marasa kyau ko kuma bayanan da ba su dace ba game da yiwuwar sake lashe zaɓe.

Source: Facebook
Dr Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV a shirin Politics Today.
'Tinubu zai iya rasa jihohi da dama'
Shugaban na PRP ya yi ikirarin cewa idan aka gudanar da zaɓen 2027 cikin gaskiya da adalci, Tinubu zai sha kaye a jihohi da dama.
Ya ce wasu daga cikin mutanen da ke kusa da shugaban ƙasar na yaudararsa da cewa tuni ya yi nasara a zaɓen da ba a gudanar ba.
Baba-Ahmed ya kuma yi zargin cewa tarukan yaƙin neman zaɓen APC ba su nuna ainihin goyon bayan da jam'iyyar ke da shi ba, yana mai cewa ana biyan wasu mutane kuɗi domin su halarci tarukan.
Ya bayyana cewa ana tattaro mutane, a ba su kuɗi sannan a kai su wuraren taron domin nuna cewa jam'iyyar na da dimbin magoya baya.
Ya buƙaci INEC da kotuna su yi adalci
Baba-Ahmed ya ce yana fatan za a gudanar da zaɓen cikin gaskiya domin makomar ƙasar da al'ummarta, musamman 'ya'yan da za su gaji ƙasar.
Ya yi kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta tabbatar da cewa dukkan jam'iyyun siyasa sun samu dama iri ɗaya a zaɓen.

Source: Facebook
Haka kuma, ya buƙaci ɓangaren shari'a da ya yi adalci wajen sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe, yana mai cewa kotuna na yanke hukunci kan kaso mai yawa na takaddamar zaɓe a ƙasar.
'Yan adawa za su yi taro
A wani labarin, kun ji cewa ana sa ran manyan 'yan siyasar adawa, ciki har da Atiku Abubakar, Peter Obi da Seyi Makinde, za su gana a Abuja ranar Litinin domin tattauna haɗa kai gabanin zaɓen 2027.
Taron zai haɗa 'yan takarar shugaban ƙasa da shugabannin jam'iyyun adawa, yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar tsayar da ɗan takara guda domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu.
Sai dai jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce tattaunawar ba ta isa ta firgita ta ba, tana mai cewa tana da kwarin gwiwar shugaba Tinubu zai sake lashe zaɓe.
Asali: Legit.ng

