"Shugaba Tinubu Ya Kunyata 'Yan Adawa, Ya Nuna Karfin da Yake da Shi a Arewacin Najeriya"

"Shugaba Tinubu Ya Kunyata 'Yan Adawa, Ya Nuna Karfin da Yake da Shi a Arewacin Najeriya"

  • Fadar shugaban ƙasa ta ce kamfen ɗin jam'iyyar APC a Arewa ya wargaza zargin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi da ƙarfi a yankin
  • Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce jam’iyyar ta nuna ƙarfin iya tara magoya baya a faɗin Najeriya
  • Onanuga ya yi hasashen cewa Tinubu zai lashe zaɓen shugaban kasa da za a yi a ranar 16 ga Janairu, 2027 da gagarumin rinjaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Fadar shugaban ƙasa ta ce jam’iyyar APC ta kunyata masu sukar ƙarfin siyasar Shugaba Bola Tinubu a Arewacin Najeriya ta hanyar gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓe a yankin da sauran sassan ƙasar.

Fadar ta ce kamfen ɗin jam’iyya mai mulki ya wargaza ikirarin da aka yi kafin zaɓe cewa APC za ta sha wahala wajen gudanar da kamfen a Arewa, kafa allunan tallata Tinubu da kuma tara magoya baya.

Kara karanta wannan

Uba Sani ya fadi abin da zai hana Arewa karbar mulkin Najeriya a 2027

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin yakin neman zaben APC a jihar Kebbi Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Alhamis.

Yadda Tinubu ya kunyata yan adawa

Ya ce gangamin yakin neman zaben da APC ta shirya a jihohin Arewa sun kunyata masu sukar Tinubu, yana mai cewa suk maganganun da yan adawa ke yadawa sun zama karya.

Onanuga ya bayyana ayyukan kamfen ɗin APC a Arewa a matsayin wani babban ƙarfafa gwiwa ga Tinubu, yana mai cewa jam’iyyar ta nuna tana iya tara magoya baya fiye da yankunan da aka saba ɗauka a matsayin cibiyoyinta na siyasa.

“Wannan wani babban saƙo ne daga Arewacin Najeriya zuwa ga Shugaba Tinubu,” ya rubuta.

APC ta karyata zarge-zargen yan adawa

Ya tuna da abin da ya kira farfagandar da aka yaɗa kafin fara kamfen, wadda ta nuna cewa APC ba za ta iya gudanar da ingantaccen yaƙin neman zaɓe a Arewa ba.

Kara karanta wannan

'Matsalar da Atiku zai ci karo da ita a yankinsa na Arewa maso Gabas'

A cewarsa, ayyukan kamfen ɗin jam’iyyar ba wai sun karyata waɗannan zarge-zarge a Arewa kaɗai ba ne, sun kuma nuna ƙarfin APC a faɗin ƙasar.

“Gangamin kamfen ɗin jam'iyya APC mai mai mulki ya kunyata su baki ɗaya, ba a Arewa kaɗai ba, har ma a faɗin ƙasarnan,” in ji Onanuga.
Onanuga.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Onanuga ya samu kwarin gwiwa

Hadimin shugaban ƙasar ya bayyana kwarin gwiwarsa kan damar Tinubu a zaɓe, inda ya yi hasashen cewa shugaban ƙasar zai samu gagarumin rinjaye.

“A ranar 16 ga Janairu, Shugaba Tinubu zai lashe zaɓen da gagarumin rinjaye,” in ji Bayo Onanuga.

Tinubu ya bukaci kabilar Igbo su zabi APC

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa ya ji haushi lokacin da wasu ’yan ƙabilar Igbo suka ƙi zaɓensa a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Tinubu ya kuma buƙaci ’yan Igbo da ke Legas su zaɓe shi, ɗan takarar gwamnan APC, Obafemi Hamzat, da sauran ’yan takarar jam’iyyar a zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262