An kara samun jihar Arewa da annobar korona ta kare, an sallami dukkan ma su jinya

An kara samun jihar Arewa da annobar korona ta kare, an sallami dukkan ma su jinya

A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Sokoto ta fitar da sanarwar cewa dukkan ma su dauke da kwayar cutar korona a jihar sun warke sarai.

Hakan na kunshe ne a cikin wani takaitaccen sako da ma'aikatar lafiya ta jihar Sokoto ta wallafa a shafinta da ke manhajar Tuwita.

A cikin sanarwar, gwamnatin jihar ta sanar da cewa an sallami sauran mutane biyar da ke zaman jinyar cutar korona a cibiyar killacewa domin su koma gidajensu, wurin iyalansu.

Mutane 116 ne aka tabbatar da cewa sun kamu da kwayar cutar korona a jihar Sokoto tun bayan bullar cutar, mutane 14 ne cutar ta yi sanadiyar mutuwarsu.

A kwanakin baya ne gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da cewa babu sauran mai dauke da kwayar cutar korona a jihar bayan ta sallami sauran mutanen da ke zaman jinya a cibiyar killacewa.

Kazalika, a ranar Alhamis, gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ta na daf da sanar da ganin bayan cutar korona.

Hakan ya biyo bayan raguwar adadin ma su kamuwa da cutar da ake samu a sanarwar da NCDC ke fitarwa kowacce rana.

An kara samun jihar Arewa da annobar korona ta kare, an sallami dukkan ma su jinya
Gwamnan jihar Sokoto; Aminu Waziri Tambuwal
Asali: Twitter

A wani labarin mai nasaba annobar korona, gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni, ya tabbatar da mutuwar mutum hudu cif a jihar sakamakon annobar korona.

Gwamnan ya bada wannan sanarwar ne a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa, yayin taron da kwamitin yaki da cutar na jihar ya gudanar.

DUBA WANNAN: Abinda kakakin gidan yari ya fada a kan halayyar Orji Kalu yayin zamansa a kurkuku

Kamar yadda gwamnan ya bayyana cikin alhini, ya sanar da mutuwar mutum hudu, wanda suka hada da dan majalisar jihar mai wakiltar Nasarawa ta yamma, daga cikin jimillar mutum 90 da suka kamu da cutar coronavirus a jihar.

Gwamnan ya kara da cewa, "samfur 705 aka kai wa hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya tun bayan da aka fara gwajin.

"Daga cikin samfur 705 da aka kai mun samu sakamakon 658 wanda daga cikinsa ne aka tabbatar da cewa mutane 90 na dauke da cutar yayin da sauran suke lafiya kalau.

"Wadanda ke karbar maganin cutar korona a cibiyoyin killacewa na fadin jihar nan na samun sauki," Sule ya kara da cewa.

Gwamnan ya tabbatar wa da jama'ar jihar cewa gwamnatinsa za ta bai wa walwala, lafiya da tsaro fifiko, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel