Yadda Ƴan APC Suka Ci Dalolin Atiku amma Suka Zaɓi Buhari a 2015
- Adams Oshiomhole ya yi zargin cewa wakilan Edo sun karɓi dalolin Atiku a zaɓen fitar da gwani na APC na 2015 amma suka zaɓi Buhari
- Adams Oshiomhole ya ce Bola Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar Muhammadu Buhari a zaɓen fidda gwani na APC a 2015
- Tsohon gwamnan Edo ya bayyana cewa shi da Fashola ne kaɗai daga cikin gwamnonin da suka amfana da goyon bayan Tinubu har yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya yi magana kan abin da ya faru a zaɓen fitar da gwanin APC a 2015.
Oshiomhole ya yi zargin cewa wakilan jihar Edo sun karɓi kuɗaɗen daloli daga hannun Atiku Abubakar a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a 2015, amma suka zaɓi Muhammadu Buhari.

Source: Facebook
Oshiomhole ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin bikin ƙaddamar da littafin From AD to APC, cewar Vanguard.
Yadda Atiku ya fafata da Buhari
Ya ce Atiku ya fafata da Buhari a zaɓen fidda gwani, inda ya raba daloli ga wakilai, ciki har da na Edo, amma duk da karɓar kuɗin, ba su zaɓe shi ba.
Tsohon gwamnan ya kuma ambaci tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, wanda shi ma ya fafata da Buhari, yana mai cewa siyasar yankin Arewa ta taka rawa a takarar.
Oshiomhole ya ce Tinubu ya tsaya tare da Buhari, inda ya shawarci mambobin tsohuwar jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) su mara masa baya a zaɓen fidda gwani.
Ya ƙara da cewa Buhari bai kashe daloli wajen neman tikitin ba, amma tawagar ACN ta tabbatar da cewa ta ba shi cikakken goyon bayanta.
A cewarsa, goyon bayan da Tinubu ya tattara daga mambobin ACN ne ya taimaka wajen tabbatar da nasarar Buhari a zaɓen fidda gwanin na APC.
Oshiomhole ya kuma tuna yadda Buhari ya yi tunanin zaɓen mataimakin shugaban ƙasa, yana mai cewa tsohon shugaban ƙasar ya yarda cewa masu kallonsa a matsayin mai tsattsauran ra'ayin addini ba za su canja ra’ayinsu ba ko da ya zaɓi Kirista a matsayin mataimaki.
Ya ce daga ƙarshe Buhari ya saurari shawarwarin iyalinsa na siyasa, inda Tinubu ya taimaka wajen samar da mutumin da ya zama mataimakin shugaban ƙasar, daga baya kuma ya fafata da shi a zaɓen fidda gwani.

Source: Getty Images
Alakar Tinubu da Fashola a Legas
Da yake magana kan Bola Tinubu, Oshiomhole ya ce shugaban ƙasar ya taɓa sukar yadda ya zaɓi wanda zai gaje shi a matsayin gwamnan Edo.
Sai dai ya yi zargin cewa wasu tsofaffin gwamnoni da suka amfana da goyon bayan Tinubu sun juya masa baya, inda ya ce shi da tsohon gwamnan Legas, Babatunde Fashola ne kaɗai suka ci gaba da nuna masa biyayya.
A ƙarshe, Oshiomhole ya danganta nasarar Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa da taimakon Allah, yana mai cewa Ubangiji ne ya kawar da matsalolin da suka taso masa tare da haifar da rikice-rikice a tsakanin 'yan adawa.
Ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa cewa Tinubu zai sake lashe zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa, yana mai cewa sake zaɓensa zai amfani Najeriya.
Radda ya bukaci kare tarihin Buhari
Mun ba ku labarin cewa Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya yi kira ga al’ummar Daura su mara wa Shugaba Bola Tinubu da jam'iyyar APC baya a zaɓe mai zuwa.
Ya buƙaci su kare tarihin marigayi Muhammadu Buhari ta hanyar zaɓen jam’iyyar mai mulki, domin dorawa daga inda marirgayin ya tsaya.
Gwamna Radda ya bayyana takarar Yusuf Muhammadu Buhari, ɗan marigayi shugaban ƙasar, a matsayin muhimmin lamari ga martabar Daura.
Asali: Legit.ng


