Buratai bai koma jihar Katsina ba - Rundunar soji
Rundunar sojin Najeriya ta ce babban hafsan rundunar sojojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya ziyarci jihar Katsina domin gani da shaida irin shirin da sansani da bataliyar soji su ka yi na yaki da 'yan bindiga.
A cewar rundunar soji, Buratai bai koma Katsina ba saboda yawaitar hare - haren 'yan bindiga a jihar da jihohin Sokoto da Zamfara.
Ana tsammanin Buratai zai kasance a jihar Katsina na tsawon lokacin bikin ranar sojoji wanda za a fara ranar Laraba, 01 ga wata, har zuwa ranar Litinin, 06 ga watan Yuli.
A baya Buratai ya shirya yin bikin ne a Jos, babban birnin jihar Filato, amma daga baya ya sauya zuwa jihar Katsina domin karawa dakarun soji karfin gwuiwar yaki da 'yan bindiga da sauran 'yan ta'adda da ke jihohin arewa maso yamma.
Tuni kwalliya ta fara biyan kudin sabulu a atisayen 'Sahel Sanity' da rundunar soji ta kaddamar a yankin arewa ma so yamma.
Kaddamar da atisayen da rundunar soji ta yi ba zai rasa nasaba da umarnin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar na kawo karshen 'yan ta'adda da aiyukan ta'addanci a jihohin arewa ma so yamma, musamman Katsina, Sokoto da Zamfara.
A yau, Laraba, ne Buratai ya bude babban sansanin sojoji na musamman a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
Samar da sansanin na daga cikin bikin zagayowar ranar dakarun sojin sama na 2020, wanda ake yi a jihar Katsina don yakar 'yan bindiga da dukkan matsalolin tsaro da suka addabi yankin arewa maso yamma.
Buratai yace: "Za a kaddamar da manyan aiyuka a yankunan kasar nan shida. Ana yin haka ne don inganta dangantakar da ke tsakanin farar hula da soji.
DUBA WANNAN: 'Babu batun sulhu': Buratai ya aiko sako da babbar murya ga 'yan bindigar Katsina, Sokoto, da Zamfara
"Dakarun za su raba kayan tallafi ga mabukata a fadin jihohi 36 na kasar harda babban birnin tarayyar kasar."
Buratai ya kara da cewa za a kaddamar da sabon atisaye mai suna SAHEL SANITY wanda amfaninsa shine yakar ayyukan 'yan bindiga da dukkan masu laifi a fadin arewa maso yamma.
Ya ce a bikin wannan shekarar, ba za a yi da tsofaffin soji ba saboda gudun barkewar annobar. Ya ce za a fitar da lokacin da ya dace don bikin jinjina musu bayan annobar.
Ya yi watsi da zargin da ake yi na cewa dakarun basu amsa kiran gaggawa idan aka yi musu a yankunan da babu zaman lafiya, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ya yi jan kunne a kan siyasantar da tsaron Najeriya baki daya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng