Yadda wani mutum ya dirkawa yarinya ciki, ya jefar jaririn a daji
- Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta damke wani mutum mai suna Shuaibu Aliyu a kan zarginsa da ake da dirkawa yarinya mai shekaru 14 ciki
- Bayan fyaden da yayi mata kuma ta haife cikin da ya shiga, ya karba jaririn inda ya jefar da shi a dajin kauyen Gidan Boka da ke karamar hukumar Wamakko
- Tuni 'yan sanda suka damke shi kuma ya amsa laifinsa. Sun shaida cewa ana kammala bincike za a mika shi gaban Kuliya
Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta kama wani mutum mai suba Shuaibu Aliyu sakamakon zarginsa da ake da dirkawa yarinya mai shekaru 14 ciki tare da yadda jaririyar da ta haifa a daji.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Sani Kaoje ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai bayan kama masu laifi.
Ya ce an damke wanda ake zargin da laifin fyade da kuma yunkurin kisan kai.
Kaoje ya bayyana cewa, "wani Alhaji Hamisu Abubakar da ke yankin Kalambaina a karamar hukumar Wamakko ta jihar Sokoto ya kai korafi ofishin 'yan sanda.
"Ya ce wani mutum mai suna Shuaibu Aliyu ya ja yarinya mai shekaru 14 cikin dakinsa inda yayi mata fyade."
Ya kara da cewa, "Sakamakon hakan, ta samu ciki har ta haihu. Ta kai wa wanda ake zargin jinjirin tare da wani abokinsa Nasiru Attahiru wanda yanzu ake name.
"Sun karba tare da jefar da jinjirin a wani daji da ke kauyen Gidan Boka a karamar hukumar Wamakko ta jihar Sokoto."
KU KARANTA: Tumbur: Bidiyon fasto yana kokarin lalata da matar aure
Kwamishinan 'yan sandan ya kara da cewa wani mutumin kirki ne ya tsinta jinjirin tare da sanar da 'yan sanda.
Ya ce an damke wanda ake zargin kuma ya amsa laifinsa.
Kwamishinan 'yan sandan ya ce ana kokarin kamo dayan wanda ake zargin.
Ya ce har yanzu ana ci gaba da bincike a kan al'amarin kuma za a mika su gaban kuliya bayan an kammala.
A wani ci gaba na daban, kwamishinan 'yan sandan ya ce wani Ahmed Alhaji Dahiru Maibuhu da ke yankin Rumbukawa ta jihar Sokoto ya ja yarinya mai shekaru 12 cikin shagonsa da ke Illela inda yayi lalata da ita.
An kama wanda ake zargin kuma ya amsa laifinsa, cewar kwamishinan 'yan sandan.
Ya kara da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya bayan an kammala bincike.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng