An Sako Peter Obi a Gaba, ana So Ya Janyewa Tinubu Takarar 2027

An Sako Peter Obi a Gaba, ana So Ya Janyewa Tinubu Takarar 2027

  • Shugaban Hukumar Bincike da Bunƙasa Albarkatun Ƙasa (RMRDC), Farfesa Nnanyelugo Ike-Muonso, ya bukaci Peter Obi ya janye takararsa ta shugaban ƙasa a 2027
  • Ike-Muonso ya kuma bukaci ’yan Najeriya su goyi bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu domin ya samu damar ci gaba da aiwatar da manufofinsa na tattalin arziki
  • A wata sanarwa da ya fitar, shugaban hukumar ya ce ya kamata Kudancin Najeriya ya kammala wa’adin mulkin shekara takwas kafin a mayar da mulki Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban Hukumar Bincike da Bunƙasa Albarkatun Ƙasa (RMRDC), Farfesa Nnanyelugo Ike-Muonso, ya kare matakin cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɗauka.

Rahotanni sun bayyana cewa Farfesa Ike-Muonso ya yi wannan kira ne yayin wata tattaunawa da ’yan jarida a Abuja ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Uba Sani ya fadi abin da zai hana Arewa karbar mulkin Najeriya a 2027

Peter Obi na NDC
Dan takarar NDC, Peter Obi. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa ya yi kira ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, da ya ajiye burinsa na neman shugabancin ƙasa, ya goyi bayan Tinubu.

Dalilin Ike kan goyon bayan Tinubu

Ike-Muonso ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba mai kishin haɗin kan Najeriya, yana mai cewa ya nuna jarumta wajen ɗaukar matakai masu wahala a fannin tattalin arziki.

Ya ce gwamnatocin baya sun kasa cire tallafin man fetur duk da matsalolin tattalin arziki, cin hanci da rashawa da kuma nauyin kuɗin da yake ɗaura wa gwamnati.

A cewarsa, cire tallafin ya ƙara yawan kuɗin shiga da ke hannun gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi, lamarin da ya taimaka musu wajen biyan albashi da sauran wajibai.

Sai dai ya amince cewa matakin ya ƙara kuɗin sufuri tare da jefa ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali, yana mai cewa gwamnati na buƙatar ƙara wayar da kan jama’a game da amfanin ƙarin kuɗaɗen shiga.

Kara karanta wannan

"Zan so ka dawo APC," Hadimin Tinubu ya aika sako ga ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027

Ya nemi Obi ya goyi bayan Tinubu

Shugaban na RMRDC ya ce ya kamata Peter Obi ya fifita haɗin kan ƙasa da zaman lafiyar siyasa maimakon ci gaba da burinsa na neman shugabancin ƙasa a wannan lokaci.

Ike-Muonso ya ce Kudancin Najeriya ya kamata ya kammala wa’adin shekara takwas na mulki kafin a mayar da shugabancin ƙasa ga Arewa.

Ya amince da gudummawar Obi wajen tattauna batutuwan kashe kuɗin gwamnati, riƙon amana da tafiyar da tattalin arziki, amma ya ce jagoranci na buƙatar sanin lokacin da ya dace mutum ya yi takara da lokacin da ya kamata ya haɗa kai da wasu.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a wajen kamfen. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya kuma bayyana cewa yana da yakinin Tinubu zai samu wa’adin mulki na biyu domin ya samu damar ƙarfafa manufofin da ya fara aiwatarwa.

Ana hasashen Tinubu zai fadi

A wani labarin, kun ji cewa shugaban jam’iyyar PRP na ƙasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasar da ya fi sauƙin kayarwa a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Bayan kamfe ya kankama, an sake neman Atiku ya janye daga takarar shugaban ƙasa a 2027

Dattijon Arewa, Hakeem Baba-Ahmed ya ce idan aka gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci, Tinubu zai sha kaye a jihohi da dama a Najeriya.

Ya kuma zargi wasu mutanen da ke kewaye da shugaban ƙasar da ba shi bayanan ƙarya kan damar da yake da ita ta sake lashe zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng