Fashola Ya Yi Bayani kan Zargin Amfani da EFCC wajen Tilasta Wa Gwamnoni Komawa APC

Fashola Ya Yi Bayani kan Zargin Amfani da EFCC wajen Tilasta Wa Gwamnoni Komawa APC

  • Tsohon gwamnan Legas, Babatunde Fashola, ya yi magana kan zargin cewa an yi amfani da EFCC wajen matsa wa gwamnonin adawa su koma APC
  • Fashola ya ba da labarin yadda wani gwamna ya nemi ya koma jam’iyyarsu a matsayin sharadin mayar da kadarar gwamnati ga jihar Legas
  • Ya ce ya ƙi amincewa da sharadin, inda ya bayyana cewa gara a ƙwace kadarar da ya sauya matsayinsa na siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Tsohon gwamnan Legas, Babatunde Raji Fashola, ya tsoma baki kan zargin cwwa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na amfani da EFCC wajen matsa wa gwamnonin adawa su sauya sheƙa zuwa APC mai mulki.

Fashola ya ba da labarin yadda ya ƙi amincewa da wani yunƙuri na matsa masa ya koma wata jam’iyyar siyasa a lokacin da yake gwamnan Legas.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: NDC ta tsoma baki kan zarge zargen da Gwamna Abba ya ɗorawa Kwankwaso

Fashola.
Tsohon ministan wutar lantarki, ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola Hoto: Babatunde Fashola
Source: Facebook

Tsohon gwamnan ya yi wannan magana ne yayin wata hira ta musamman da tashar ARISE News ranar Juma’a, 27 ga watan Nuwamba, 2026.

Tambayar da aka yi wa Fashola

A yayin hirar, an tambaye shi ko an matsa wa gwamnonin da suka sauya sheƙa zuwa APC lamba ne har suka bar tsoffin jam’iyyunsu.

Mai tambayoyin ya ambaci bayanin da gwamnan jihar Zamfara ya yi na cewa ya koma APC ne domin samun damar yin aiki kafada da kafada da gwamnatin tarayya.

Haka kuma, ya kawo zargin da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi a baya-bayan nan cewa gwamnatin Tinubu na amfani da EFCC wajen yi wa gwamnonin adawa barazana domin tilasta musu shiga jam’iyya mai mulki.

Fashola ya bada amsa da labari

A martaninsa, Fashola ya ba da labarin wani abu da ya faru a lokacin da yake gwamnan Legas, inda ya ce an yi ƙoƙarin matsa masa ya koma wata jam’iyyar siyasa a matsayin sharadin mayar da wata kadarar gwamnati ga jihar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nuna damuwa kan ɗalibai 78 da aka sace, ya ɗauki alƙawari mai girma

Ya tuna cewa gwamnatinsa ta sha neman a mayar wa jihar Legas da babban ginin da ke Lagos House, Marina, inda Shugaban Ƙasa ya kasance yana zama a baya.

A cewarsa, yayin wata ganawa da wani tsohon Shugaban Ƙasa da bai bayyana sunansa ba, wani gwamna, wanda a yanzu sanata ne a APC, ya ba da shawarar cewa ba za a mayar wa jihar Legas da ginin ba sai idan ya amince ya koma jam’iyyarsu.

Fashola ya ce ya ƙi amincewa da wannan sharadi, inda ya jaddada cewa gara ya rasa kadarar da ya ci amanar akidarsa ta siyasa.

Ya ce:

“A lokacin ni ne kaɗai gwamnan AC, kuma ni ne matashin gwamna. Sai na ce, ‘Mai girma Shugaban Ƙasa, idan wannan ne sharadin, ku riƙe gidan.’
Fashola.
Tsohon ministan makamashi, ayyuka da gidaje, Babtunde Fashola tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Babatunde Raji Fashola
Source: Facebook

Yadda Fashola ya samu matsala da gwamnati

Fashola ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta samu saɓani da gwamnatin tarayya a kan wasu ayyuka da batutuwa daban-daban, amma duk da haka ta ci gaba da kasancewa a jam’iyyarta ta siyasa.

"Don haka ina so ku fahimta. Ko sun matsa maka ko ba su matsa maka ba, kai ne zaka nci. Akwai abubuwa da yawa da na so gwamnatin tarayya ta yi a wancan lokacin amma suka ƙi yarda," in ji shi.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, El Rufai ya tsage gaskiya a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu

Fashola ya yaba wa tsarin Tinubu

Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Legas, Babatunde Fashola ya bayyana dalilin da ya sa Bola Tinubu ya fi Atiku da Peter Obi damar lashe zaben shugaban kasa na 2027.

Fashola ya ce yadda shugaban kasar ke iya rike mutanen da suka yi aiki tare da shi tare da jawo tsofaffin abokan hamayyarsa cikin tafiyarsa ta siyasa, ya ba shi fifiko kan sauran masu neman kujerar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262